Miliyan N100m na Fom: Yan Najeriya na gudanar da rayuwar ƙasaita, Kakakin APC

Miliyan N100m na Fom: Yan Najeriya na gudanar da rayuwar ƙasaita, Kakakin APC

  • Yayin da ake ta kai kawo kan kuɗin Fam ɗin tsayawa takara da APC ta sanya, jam'iyyar ta bayyana abun da yasa ta zabga kuɗi
  • Kakakin APC na ƙasa, Mista Felix Morka, ya ce jam'iyya ta san halin da tattalin arziki yake a ko ina kuma ta duba haka kafin yanke hukunci
  • A cewarsa, a halin yanzun mutane na samun kudi a ɓagas ba tareda wahala ba, kuma suna gudanar da rayuwar ƙasaita

Abuja - Jam'iyyar APC ta faɗi dalilin da yasa ta zabga kuɗin sayen Fom ɗin nuna sha'awar takara karkashinta a babban zaben 2023 dake tafe.

Jaridar Punch ta rahoto cewa APC zata buɗe siyar da Fom ɗin tsayawa takarar shugaban ƙasa, gwamna, da yan majalisun ƙasa da na jihohi a ranar Asabar mai zuwa.

Kakakin APC na ƙasa, Felix Morka, wanda ya sanar da matakin, ya ce jam'iyya zata sayar da Fom ɗin takarar shugaban ƙasa miliyan N100m na gwamna kuma miliyan N50m.

Kara karanta wannan

Ina da kwarin guiwa da izinin Allah wannan ɗan takarar ne zai gaji Buhari a 2023, Sanatan Kano ya magantu

Kakakin APC na ƙasa, Felix Morka.
Miliyan N100m na Fom: Yan Najeriya na gudanar da rayuwar ƙasaita, Kakakin APC Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Yayin da ya bayyana a wani shirin kafar watsa labarai ta Channels tv ranar Laraba da daddare, Morka ya ce Farashin kuɗin Fam, "ba su yi tsada ba."

A cewar mai magana da yawun APC mai mulki, mutane na samun kudi cikin sauƙi a Najeriya kuma suna gudanar da rayuwar ƙasaita.

A kalamansa ya ce:

"Farashin ya yi tsada ga masu hangen kujera lamba ɗaya? Nasan mutane za su yi tambaya irin wannan, amma ka da ku mance wasu rukunin mutane na musamman an duba su. Matasa tsakanin shekara 25-40 an rage musu kashi 50."
"Zamani ya kawo mu muna rayuwa a ƙasar nan inda zaka ga mutane na gudanar da rayuwar jin daɗi da ƙasaita kuma suna samun kuɗaɗen shiga a sauƙaƙe."

Ko jam'iyyar APC ta zama ta masu kuɗi ne?

Kara karanta wannan

2023: Ɗan takarar shugaban ƙasa a APC ya kaɗu da jin kuɗin fam Miliyan N100m

Yayin da aka tambaye shi ko jam'iyyar APC ta koma jam'iyyar masu kuɗi, Kakakin APC ya ba da amsa da cewa:

"Ba haka bane, a ɓangaren tattalin arziki komai ya lalace, ba'a Najeriya kaɗai ba ko wace ƙasa kaje. Shin kana tunanin akwai wata ƙasa da tattalin arzikinta bai taɓu ba, Amurka zaka ce ko Burtaniya?"
"Matakin da muka ɗauka ya yi dai-dai da halin da ake ciki, jam'iyya na ganin wannan farashin bai yi yawa ba."

A wani labarin na daban kuma Na hannun daman gwamna Ganduje ya canza shawara, ya janye daga takarar gwamna a 2023

Sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji, ya janye daga tseren takarar gwamnan jihar a zaɓe mai zuwa.

Bayanai sun nuna cewa Alhaji ya ɗauki wannan matakin ne biyo bayan gana wa da mai girma gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel