2023: Wike Ya Sanar Da Abu Ɗaya Tak Da Zai Iya Sa Ya Janye Wa Wani Takarar Da Ya Ke Yi a PDP

2023: Wike Ya Sanar Da Abu Ɗaya Tak Da Zai Iya Sa Ya Janye Wa Wani Takarar Da Ya Ke Yi a PDP

  • Nyesome Wike, gwamnan Jihar Rivers kuma dan takarar shugaban kasa a PDP ya magantu kan batun sasanci a takarar shugaban kasa
  • Wike ya ce idan ba mutuwa ya yi ba, ba bu wani dalilin da zai saka shi ya janye wa wani dan takarar shugaban kasar a PDP gabanin babban taron jam'iyyar
  • Gwamnan na Rivers ya yi ikirarin cewa mutanen da ke maganan cewa a zo a yi sasanci suma kansu hannunsu ba tsafta bane da shi don haka kawai a fafata a zaben fidda gwani

Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike, ya dage kan cewa ba zai janye wa kowa ba game da batun takarar shugaban kasa gabanin zaben 2023.

Wike, wanda dan takarar shugabancin kasa ne a jam'iyyar PDP ya furta hakan ne yayin wata hira da BBC Pidgin ta yi da shi.

Kara karanta wannan

2023: Shehu Sani ya hango yadda APC da PDP za su zabi 'yan takarar shugaban kasa

2023: Wike Ya Sanar Da Abu Ɗaya Tak Da Zai Iya Sa Ya Janye Wa Wani Takarar a PDP
2023: Mutuwa Ce Kadai Za Ta Sa In Janye Wa Wani Takarar Shugaban Kasa, Wike. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

The Punch ta rahoto yadda wasu jiga-jigan jam'iyyar na PDP suka bukaci cewa a zabi dan takarar jam'iyyar ta hanyar sasanci.

Idan ba mutuwa ba, ba abin da zai sa in janye wa wani takara a PDP, Wike

Amma, Wike ya ce mutuwa ne kawai za ta saka shi ya janye wa wani dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben na 2023.

Da aka tambaye shi ko akwai wani dan takarar da zai iya janye wa, Wike ya ce:

"Don mene zan janye wa wani? Idan kuna son sasanci, ya zama dole akwai adalci da daidaito a jam'iyyar. Shin hannun wadanda ke neman sasancin yana da tsafta? Mutanen da ke maganan sasanci ne ke tafiyar da zaben. Shin abin da jam'iyyar ke so kenan?

Kara karanta wannan

Kada kowa yazo da waya: Aisha Buhari ta shirya liyafa ga 'yan takarar shugaban kasa a dukkan jam'iyyu

"Ba jam'iyya ke magana ba. A siyasa, akwai abu da ake kira 'shine shine bobo. A yayin da kake kwallara ido, ba zaka ga komai ba. Wasu na zaton za su min wayau. Yaudara ce. Bana son mayaudara a rayuwa ta."

Ya cigaba da cewa:

"Abin da kadai zai sa in janye wa wani dan takarar PDP shine mutuwa. Idan ina da rai, za mu fafata, za mu yi zaben fidda gwani a ranar 28/29 na Mayu."

A ranar Talata, Wike ya gargadi shugabannin PDP kan nada deliget wadanda suka hada kai da wasu yan takarar a kwamitin zaben fidda gwanin.

Ba A Ga Atiku Ba A Taron Da Wike Ya Yi Da Masu Neman Takarar Shugaban Ƙasa Na Jam'iyyar PDP

A wani labarin, Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya bai halarci taron sirrn da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya shirya ba tare da wasu ‘yan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP ba, yayin da zaben fidda gwanin jam’iyyar ya ke karatowa.

Kara karanta wannan

Kofar rashawa: 'Yan Najeriya sun kadu da jin farashin fom din takarar shugaban kasa N100m a APC

An tattaro yadda ‘yan takarar suka dade suna tattaunawa dangane da wanda zai tsaya takara don gudun tashin tarzoma ta cikin jam’iyyar yayin zaben, The Nation ta ruwaito.

‘Yan takarar da suka halarci taron da aka yi gidan gwamnati da ke Port Harcourt sun hada da Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed; Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal; tsohon manajan darekta na bankin kasa da kasa na FSB, Dr. Mohammed Hayatu-Deen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164