2023: Kwana Kaɗan Bayan Buhari Ya Musu Afuwa, An Yi Kira Ga Dariye Da Nyame Su Fito Takarar Shugaban Ƙasa
- Wani dan takarar shugaban kasa daga yankin tsakiyar Najeriya, Moses Ayom, ya mika roko ga tsaffin gwamnonin da aka samu da laifin sata
- A baya bayan nan ne Shugaba Muhammadu Buhari ya yi afuwa ga tsaffin gwamnonin na Jihohin Taraba da Plateau
- A cewar Ayom, yin takarar Nyame da Dariye a matsayin yan takarar shugaban kasa zai taimakawa yankin wurin fitar da shugaban kasa
An bukaci tsaffin gwamoni - Jolly Nyame da Joshua Dariye - wadanda a baya-bayan nan Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa afuwa su shiga takarar shugaban kasa.
Dan takarar shugaban kasa daga yankin tsakiya a Najeriya, wato Middle Belt, Moses Ayom, ne ya yi wannan kirar a ranar Alhamis 21 ga watan Afrilu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
The Nation ta rahoto cewa Ayom, wanda shima dan takarar shugaban kasa ne a karkashin jam'iyyar APC ya yaba wa Shugaba Buhari bisa afuwar da ya yi wa tsaffin gwamnonin na Taraba da Plateau.
The Punch ta rahoto cewa Ayom ya ce shigar Nyame da Dariye cikin takarar zai bunkasa damar yankin na fitar da shugaban kasa.
Neman ganin yankin Tsakiya ta shiga siyasa gadan-gadan
Da ya ke cewa tsaffin gwamnonin da aka yanke wa laifin sun fuskanci hukuncin saboda sun fito daga kananan kabilu ne, Ayom ya ce akwai shugabanni daga wasu kabilun da dama da suka yi sata fiye da nasu amma ba a tura su kurkuku ba.
Kalamansa:
"Karin yawan yan takarar daga kananan kabilun zai taimaka mana wurin samun nasara ko na samun kujerar shugaban kasa ko mataimaki."
Nyame Da Dariye: Ka Janye Afuwar Ko Mu Kaɗa Maka Ƙuri'ar Rashin Gamsuwa, Ƙungiyoyin Arewa 19 Sun Gargaɗi Buhari
Ayom ya kuma ankarar da mutanen yankin Tsakiya kan wani bita da kuli da yan siyasa ke yi na tsauwala kudin fom din takara ta yadda yan takara masu gaskiya ba za su iya siya ba.
Ba a Taɓa Gwamnatin Da Ta Kai Ta Buhari Rashawa Ba: Naja'atu Ta Ragargaji Buhari Kan Yafewa Dariya Da Nyame
A wani rahoton, Naja’atu Mohammed, mamba a Hukumar Dauka da Ladabtar ‘Yan sanda, PSC, ta caccaki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan yafe wa tsofaffin gwamnoni, Joshua Dariye na Jihar Filato da Jolly Nyame na Jihar Taraba.
Daily Nigerian ta ruwaito yadda a ranar Alhamis, majalisar jiha, wacce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta ta yafe wa Dariye da Nyame tare da wasu fursinoni 157 da ke fadin kasar nan.
An yanke wa Dariye, wanda ya rike kujerar gwamnan Jihar Filato tsakanin 1999 da 2007, shekaru 14 a gidan yari saboda satar N1.16b, sannan an yanke wa Nyame shekaru 12 a gidan yari akan satar N1.6b, wanda ya yi gwamnan Jihar Taraba tsakanin 1999 da 2007 a shekarar 2020.
Asali: Legit.ng