INEC ta karyata Tinubu a karo na 2 a wata 1, ta yi wa jigon APC martani kan batun katin zabe
- Hukumar zabe mai zaman kanta ta karyata ikirarin cewa katin zabe na PVC su na iya daina aiki
- Farfesa Mahmood Yakubu ya tabbatar da haka, yayin da yake bayanin inda hukumar INEC ta kwana
- An sake jin Bola Tinubu yana fadawa mutane cewa katin PVC su kan tashi daga aiki idan sun tsufa
Abuja - Shugaban hukumar zabe mai zaman kan ta, Farfesa Mahmood Yakubu ya yi karin haske a game da wani jita-jita da ke ta faman yawo a kasar nan.
Jaridar Daily Trust ta rahoto Farfesa Mahmood Yakubu yana musanya ikirarin cewa katin kada kuri’a watau PVC ya kan tashi daga aiki idan har ya dade.
Da yake jawabi a garin Abuja a ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu 2022, shugaban hukumar zaben na kasa ya ce katin ba su da ranar daina aiki a Najeriya.
Mahmood Yakubu ya ba masu zabe tabbacin cewa za'a yi amfani da PVC a wajen kowane zabe.
Bugu da kari, Farfesa Yakubu ya ce duk wanda suka yi rajista tsakanin watan Junairu zuwa Maris na shekarar nan za su samu katinsu kafin ayi zaben 2023.
Haka zalika duk wanda ya kammala rajistar samun katin zabe kafin cikar lokacin da hukumar ta bada, zai samu damar kada kuri’a a zaben shekara mai zuwa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Za a iya canza wurin zabe
An rahoto shugaban na INEC yana cewa masu bukatar canza inda za su yi zabe, za su iya yin wannan a kowane ofishin hukumar da ke a fadin kasar nan.
Yakubu ya yi kira ga wadanda suka jefar da katinsu na PVC ko kuma katin ya lalace, da su nemi ayi masu sabon kati domin su iya kara kada kudi’a a 2023.
PVC za su daina aiki?
“An kawo wadannan matakai ne daidai da dokar kasa domin a biyawa ‘Yan Najeriya bukatarsu.”
“Zancen cewa katin PVC su na tashi daga aiki ba gaskiya ba ne. Don haka ana kira ga mutane su guji rajista fiye da daya, hakan ya saba dokar zabe.”
- Mahmud Yakubu
Farfesan yace duk wanda aka samu da laifin yin rajista sau biyu ko fiye zai yabawa aya zaki, domin za a iya gurfanar da shi a gaban kotu kan saba dokar zabe.
Tinubu ya hakikance
A watan Afrilun 2022 ne aka ji labari Asiwaju Bola Tinubu, ya fito ya bada hakuri a game da kuskuren da ya yi na cewa katin zaben PVC su kan daina amfani.
Wata daya da yin haka, sai aka sake jin tsohon gwamnan na Legas ya sake maimaita wannan magana. Ko a wancan lokaci, sai da hukumar INEC ta ci gyaran sa.
Asali: Legit.ng