Buhari ga shugabannin APC: Ku haramtawa PDP mulki a 2023 kamar yadda kuka yi a 2015
- Shugaba Buhari ya fadi magana mai daukar hankali ga gwamnonin APC da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyya mai mulki a taron NEC da aka yi a Abuja
- Sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ya fitar ta nuna cewa Buhari ya bukaci ‘yan jam’iyyar APC da su guji kura-kuran da suka kai ga faduwar PDP a 2015
- A wajen harkokin siyasa, shugaban na Najeriya ya kuma yi amfani da taron na NEC wajen yin magana kan kokarin gwamnatinsa na magance matsalar rashin tsaro
FCT, Abuja – Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 20 ga watan Afrilu a Abuja ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar APC da su kara lura da matsalolin da suka kai ga faduwar jam’iyyar PDP a zaben 2015.
Shugaban ya yi wannan jawabi ne a taron kwamitin zartaswar jam’iyya mai mulki ta kasa (NEC), inji mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina a wata sanarwa da Legit.ng ta gani.
A cewar Buhari:
“PDP ta yi tunanin cewa lokaci ne kawai zai iya cire su, kuma a zahiri lokacin ya yi. Sun yi tunanin ba zai yuwu su fadi zabe ba."
Shugaba Buhari ya tuno da cewa hadakar jam'iyyun ACN, CPC, ANPP wasu 'yan APGA da kuma sabuwar PDP ne suka kafa APC, wanda wani bangare ne na jam’iyya mai mulki a lokacin.
Yace:
“Mun kafa wani kwamiti mai cikakken tsarin yadda za a kawar da PDP daga mulki. PDP ta yi tunanin hakan ba zai yiwu ba. Amma abin ya faru."
Ayi aiki domin ganin an hada kan APC, Buhari ga NWC
Shugaba Buhari ya shaida wa sabbin mambobin kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na APC wajen kokarin ganin jam’iyyar ta samu hadin kai wuri guda ta hanyar samar da karin damar tattaunawa.
Ya kara da cewa:
“Babu lokacin da za mu habaka bambance-bambance a tsakaninmu. Ba mu da lokacin haka.'
Shugaban ya yabawa kwamitin CECPC karkashin jagorancin Mai Mala Buni da daukacin mambobinsa bisa sadaukar da kansu don yi wa jam’iyyar hidima.
Hakazalika, a bangare guda ya nemi 'yan jam'iyyar ta APC da su yi aiki tukuru don ganin sun ciyar da jam'iyyar gaba, kana su yi aiki don ganin PDP bata sake mulki ba.
A bangare guda, shugaba Buhari ya bayyana irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu, musamman ta fusakar tsaro, inda yace mulkinsa ya fi na Jonathan tasiri wajen kassara lagwan 'yan ta'adda.
Ga cikakkiyar sanarwar da ke bayyana batutuwan Buhari:
Wani attajiri dan jihar Kebbi ya zuge N100m don sayawa Tinubu Fom din takara
A wani labarin, Attajirin dan kasuwa dan jihar Kebbi, Aminu Sulaiman, ya zuge cheque na milyan dari don sayawa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu tikitin takara kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC.
Aminu Sulaiman, wanda shine Dirakta Janar kungiyar goyon bayan Tinubu watau Tinubu Support Organisation (TSO).
Asali: Legit.ng