Bincike: Da gaske ne Amaechi ya kai wa shugaban APC jakunkunan kudi yayin da ya ziyarcesa?

Bincike: Da gaske ne Amaechi ya kai wa shugaban APC jakunkunan kudi yayin da ya ziyarcesa?

Ba a boye aka yi ba, cewa ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya ziyarci Alhaji Abdullahi Adamu, sabon shugaban jam'iyyar APC a jihar Nasarawa.

Sai dai, ziyarar ta bar baya da kura inda zargi da hasashe masu tarin yawa suka dinga bullowa kan kokarin Amaechi na son zama shugaban kasar Najeriya na gaba yayin da yake ta tuntubar mutane a fadin kasar nan.

Bincike: Da gaske ne Amaechi ya kai wa shugaban APC jakunkunan kudi yayin da ya ziyarcesa?
Bincike: Da gaske ne Amaechi ya kai wa shugaban APC jakunkunan kudi yayin da ya ziyarcesa?. Hoto daga OluDavid Odunsi
Asali: UGC

Akwai zargin da ke ta yaduwa na cewa ministan ya isa gidan Adamu da ke Keffi dauke da jakunkunan kudi domin ya siye zuciyar shugaban APC.

Wannan zargin na gaggawa ya taso ne bayan bayyanar hoton Amaechi da Adamu inda aka ga wasu jakunkuna a bayansu.

Kamar yadda wani ma'abocin amfani da Twitter mai suna T'Challa ya bayyana, "Kun ga bashin da Buhari da Amaechi ke karbowa daga China domin gina layikan dogo dankare a jakunkunan can."

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda Ganduje ya kalli Wike ido cikin ido ya fada masa cewa ba zai kai labari ba a 2023

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani dan Najeriya mai suna Ugochukwu cewa ya yi: "Kalla Amaechi da yace baya son kudi. A bayansu jakunkunan kudi ne wadanda @ChibukeAmaechi ya kai wa shugaban APC."

Tantancewa

Sai dai, babu shaida kwakwara kan cewa jakunkunan dauke suke da kudi. Ko da kuwa kudi ne dankare a jakunkunan, babu wanda zai iya tabbatar da cewa Amaechi ne ya kai su, ballantana kuma a ce domin siye zuciyar shugaban jam'iyyar ne.

Bugu da kari a kan haka, wata Habeebah Suleiman, wacce ta yi ikirarin cewa tana cikin tawagar ministan yayin ziyarar, ta ce Amaechi bai yi ko rabin sa'a tare da Adamu ba.

Suleiman ta ce: "Wannan rashin kyautawa har ina. A jiya Asabar ina gidan shugaban APC a Keffi wunin ranar.
"A lokacin da Amaechi ya shigo, minti 20 ya yi kuma ya tafi. Babu ko jami'in tsaro daya da ya rako shi cikin gidan balle a kai ga wata Ghana Must Go."

Kara karanta wannan

Tikitin takarar shugabancin kasa: Tinubu da Amaechi na rubibin wakilan doka 3,000 na APC

Hukunci

Ikirarin cewa Amaechi ya kai ziyara gidan shugaban APC da jakunkunan kudi ba gaskiya bane kuma zargi ne da bashi da tushe balle makama.

2023: Amaechi ya fara neman shawarwari, ya ziyarci sarakunan Daura, Kano da Bichi

A wani labari na daban, ministan sufuri, Honarabul Chibuke Rotimi Amaechi a ranar Litinin, ya ziyarci sarakunan Kano da Daura domin burinsa na fitowa takarar shugabancin kasa.

Wannan ziyarar na zuwa ne bayan kwanaki biyu da ministan ya bayyana burinsa na fitowa takarar shugaban cin kasa a 2023.

Ya ziyarci sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da takwaransa na Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, a fadarsu inda ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng