2023: APC ta rasa wani babban jigonta a jihar Oyo, ya sauya sheka zuwa PDP
- Hadimin marigayi Abiola Ajimobi, Sumbo Owolabi ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP mai mulki a jihar Oyo
- Owolabi ya sauya sheka ne yan kwanaki bayan tsohon dan takarar gwamna na APC a jihar, Joseph Tegba, ya fice daga jam'iyyar
- Tuni dai dan siyasar ya sa labule da gwamnan jihar, Seyi Makinde domin kammala shirye-shiryen komawarsa PDP
Oyo - Sumbo Owolabi, tsohon kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Oyo a karkashin gwamnatin marigayi tsohon gwamna, Abiola Ajimobi, ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa Peoples Democratic Party (PDP) mai mulki a jihar.
Owolabi, wanda ya kasance tsohon shugaban karamar hukumar Ona-Ara, ya gana da Gwamna Seyi Makinde a kwanan nan domin kammala shirye-shiryen komawarsa jam’iyyar ta PDP, rahoton The Guardian.
Ya kuma kasance da ga wani babban basarake na garin Ibadan.
Sauya shekar nasa na zuwa ne yan kwanaki bayan tsohon dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Oyo, Joseph Tegba, ya sauya sheka zuwa babbar jam’iyyar adawa ta kasar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A halin da ake ciki, tsohon shugaban PDP a jihar, Alhaji Kunmi Mustapha, ya bayyana cewa sauya shekar da manyan yan siyasa ke yi zuwa cikin jam’iyyar a fadin Najeriya alamu ne da ke nuna jam’iyyar za ta karbi mulki daga APC a 2023, rahoton Nigerian Tribune.
Mustapha wanda ya kasance mai bayar da shawara na musamman ga gwamnan jihar Oyo kan harkokin jam’iyyun siyasa, ya bayyana cewa abun farin ciki ne cewa mutane kamar su Cif Joseph Tegba, tsohon jigon APC a jihar da Hon. Sunbo Owolabi, tsohon kwamishinan albarkatun ruwa sun dawo PDP.
Ya bayyana cewa yan siyasar sun gaji da gurbataccen shugabanci da gazawar gwamnatin Buhari wajen magance rashin tsaro a fadin kasar.
Abdulaziz Yari ya bayyana gaskiyar lamari game da batun sauya shekarsa daga APC zuwa PDP
A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ya bayyana rahoton sauya shekar tsaginsa zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin take gaskiya.
A ranar Lahadi ne shugaban PDP a jihar, Kanal Bala Mande mai ritaya, ya fada ma manema labarai a Gusau cewa Yari, Sanata Marafa da sauran jiga-jigan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun sauya sheka zuwa jam’iyyar adawar.
Kakakin tsagin Yari na APC, Ibrahim Magaji, ya ce shugaban na PDP a jihar ya yi gaggawa wajen sanar da batun, jaridar The Guardian ta rahoto.
Asali: Legit.ng