Kwara: Matashi ɗan shekara 38 ya shiga tseren takarar gwamnan a zaɓen 2023
- Matashi ɗan shekara 38 wanda ya jima ya na hidimta wa Bukola Saraki ya shiga tseren neman ɗarewa mulkin Kwara a zaɓen 2023
- Matashin mai suna Idris ya samu gagarumin goyon baya daga kungiyoyin matasa na jihar Kwara
- A cewa haɗakar kungiyoyin lokaci ya yi da matasa zasu karɓi ragamar mulkin jihar da kuma Najeriya baki ɗaya
Kwara - Wani matashi ɗan shekara 38 kuma tsohon hadimin Sanata Bukola Saraki, ya shiga tseren takarar kujerar gwamna a jihar Kwara a zaɓen 2023.
Ɗan takarar gwamnan ya jima tare da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, kuma ya fito ne daga ƙaramar hukumar Edu dake mazaɓar Kwara ta arewa.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ɗan takarar shi ne matashi mafi ƙarancin shekaru daga cikin mutanen da suka ayyyana neman kujerar ta gwamna.
Matashin mai suna Idris ya shiga tseren takarar ne kwanaki kaɗan bayan jam'iyyar PDP ta kai tikitin takararta zuwa yankin mazaɓar Kwara ta Arewa.
Rabon da yankin ya karɓi jagorancin jihar Kwara tun shekarar 1992 lokacin da tsohon gwamna, Shaaba Lafiagi, ke kan madafun iko a jamhuriya ta uku.
Idris zai bi sawun kakakin majalisar dokokin jihar Kwara, Injiniya Danladi Yakubu Saliu, wanda ya zama mamba a majalisa yana ɗan shekara 34 a duniya.
Matashin ya samu goyon baya
Ƙungiyoyin matasan jihar Kwara da matasa masu kwarewa sun yi kira ga jam'iyyar PDP da sauran mutanen jihar su koma bayan matashin ba tare da duba banbancin jam'iyya, ƙabila ko addini ba.
Da suke jawabi a taron manema labarai a Cibiyar NUJ dake Ilorin, haɗakar ƙungiyoyin matasan sun bayyana cewa lokaci ya yi da matasa zasu karɓi jihar.
Abdulrahman Mohammed, wanda ya yi jawabi ga manema labarai a madadin matasa, ya ce:
"Matasa na da ƙarfi, kwarewa da sauran abubuwan da ake bukata fiye da wasu dattawan ma su jagorancin Kwara da Najeriya baki ɗaya."
A wani labarin kuma Hukumar zaɓe INEC ta yi magana kan yawan mutanen dake neman takarar shugaban kasa a 2023
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa, (INEC), ta ce ƙaruwar mutanen dake nuna sha'awar tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 be dame ta ba.
INEC ta ce jam'iyyun siyasa 18 ne kacal halastattun da za su gabatar mata da yan takarar su a tseren kujera mai daraja ta ɗaya a Najeriya, kuma kowace jam'iyya ɗan takara ɗaya zata tsayar.
Asali: Legit.ng