2023: A Manta Da Batun Zaɓe Bayan Saukan Buhari, a Kafa Gwamnatin Wucin Gadi Da Za Ta Saita Najeriya, Babalola

2023: A Manta Da Batun Zaɓe Bayan Saukan Buhari, a Kafa Gwamnatin Wucin Gadi Da Za Ta Saita Najeriya, Babalola

  • Afe Babalola, Kwararren Masanin Shari'a a Najeriya, yana ganin akwai abubuwa da dama da ya kamata a yi gabanin babban zaben 2023
  • Babalola ya bada shawarar cewa a yi sabon kundin tsarin mulki kuma a kafa gwamnatin wucin gadi don yin wasu manyan canje-canje a shugabancin kasar
  • Afe Babalola shine mammalakin jami'ar ABOUD dake Eado Ekiti, babbar birnin jihar Ekiti

Ado Ekiti, Ekiti - An yi kira da cewa a kafa gwamnatin wucin gadi bayan wa'adin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari ya zo karshe a 2023.

Babban lauya kuma dattijon kasa, Afe Babalola, wanda ya yi magana a yayin wani taro a Ado-Ekiti, a ranar Litinin 18 ga watan Afrilu, 2022 ne ya yi wanan kirar, NAN ta rahoto.

2023: Kada a Yi Zaɓe Bayan Buhari Ya Sauka, a Kafa Gwamnatin Wucin Gadi, Babalola
Kada a Yi Zaɓe Bayan Buhari Ya Sauka a 2023, a Kafa Gwamnatin Wucin Gadi, In Ji Babalola. Hoto: Fadar Shugaban Kasa.
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Najeriya Ta Bada Hutun Kirsimeti Da Sabon Shekara

Babalola, yayin taron, ya kuma bada shawarar cewa a a kirkiri sabon kudin tsarin mulki a karkashin sabuwar gwamnatin, a kuma dakatar da yin babban zaben shekarar 2023, Daily Trust ta kara.

A cewar fitaccen lauyan, tsaffin shugabannin kasa da mataimakansu, wasu ministoci, gwamnoni da wakilai daga kungiyoyin kwararru ne za su jagoranci gwamnatin wucin gadin.

Kungiyoyin da ya ambata sun hada da Kungiyar Likitocin Najeriya, Kungiyar Lauyoyin Najeriya, Kungiyar Kwadago ta Kasa, Kungiyar Yan Jarida, Kungiyar Malaman Jami'o'i da Kungiyoyin Cigaban Al'umma.

Ya jadada cewa sabon kudin tsarin mulkin za ta haifar da gwamnatin tarayya na ainihi a maimakon tsarin gwamnati mai shugaban kasa.

Kalamansa:

"A karkashin sabon kundin tsarin mulkin, allawus din zama kawai za a rika biyan yan majalisu ba albashi ba.
"A samar da gwamnatin tarayya na ainihi a maimakon tsarin mulkin shugaban kasa mai tsada. Na bada shawarar a kafa gwamnati na wakilai mai majalisa kwara daya tak.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwar Kungiya Mai Hatsari Ta Ɓullo A Najeriya, Shugaban NSCDC Ya Yi Gargaɗi

"Sabon kundin tsarin mulkin ya samar da hukuma da za ta rika tantance dukkan yan takara a matakan kananan hukuma, jiha da tarayya, ta bincika hanyar samun kudinsu har da laifuka da shari'a a kotu."

2023: Za mu bi didigin inda ƴan takara suke samo kuɗi, za mu sa ido kan asusun bankin ƴan siyasa, INEC

A wani rahoton, kun ji cewa Hukumar zabe mai zaman kanta na Najeriya, INEC, ta aika da muhimmin sako ga yan siyasa da jam'iyyun siyasa gabanin babban zaben shekarar 2023.

Hukumar ta sha alwashin cewa za ta saka idanu a kan 'yan siyasa da jam'iyyun siyasa domin gano inda suke samo kudade domin yakin neman zabe, Vanguard ta ruwaito.

Shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya bayyana hakan yayin wani taro da hukumar zaben ta shirya a Abuja, ranar Juma'a 21 ga watan Janairu, kuma ya ce hukumar za ta saka ido kan yadda aka hada-hadar kudade ranar zabe don dakile siyan kuri'u, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164