Yadda yaƙin Rasha da Ukaraine ya yi mugun tasiri kan farashin kayan Gine-Gine a Najeriya

Yadda yaƙin Rasha da Ukaraine ya yi mugun tasiri kan farashin kayan Gine-Gine a Najeriya

  • Masana sun koka kan yadda farashin kayayyakin amfani wajen gine-gine suka tashi tun bayan fara yaƙin Rasha da Ukraniya
  • A cewarsu, ya kamata gwamnatin tarayya ta sake gyara a kasafin 2022 duba da Farashin kayayyaki a yanzu
  • Masana a bangaren masana'antun gine-gine sun bayyana cewa mafi yawan ayyuka na bukatar karin kashi 25 don cigaba

Yaƙin dake faruwa tsakanin ƙasar Rasha da makwafciyarta Ukraine ya shafi tattalin arziƙin ƙasashen duniya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sai dai a nan Najeriya, masana'antar gine-gine ce abun ya fi yi wa illa fiye ta kowane ɓangare.

Masana a ɓangaren, waɗan da suka zauna kwanan nan a Abuja domin duba kasafin kuɗin 2022 da kuma yadda ya shafi masana'antar, sun amince farashin kayan gini sun ƙaru a hankali a hankali tun bayan fara yaƙin.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda 'Yan Bindiga Suka Ci Karen Su Ba Babbaka, Suka Halaka Ma'aikacin INEC a Wurin Aikin Rijistar Zaɓe

Farashin kayan gini ya tashi a Najeriya.
Yadda yaƙin Rasha da Ukaraine ya yi mugun tasiri kan farashin kayan Gine-Gine a Najeriya Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Bisa wannan hujja, suka roƙi gwamnatin tarayya ta tausaya wa bangaren, ta sake yin garambawul ga kasafin kuɗin 2022 da aka ware musu domin ka da hakan ya jawo jinkiri wajen aiwatar da manyan ayyuka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Me masanan suka hango?

Shugaban masana'antar gine-gine ta ƙasa (FOCI), Injiniya Nasiru Ɗantata, ya ce hauhawar farashin ginshiƙan kayayyakin gini a baya-bayan nan, ya zama abun damuwa ga mambobinsa.

Ya ce:

"A tsakanin watan Janairu zuwa Maris 2022, Farashin kayayyakin sun tashi daga asalin farashin su na baya."
"Yanzu, hauhawar farashin Siminti da Man Fetur ya nunka biyu, wasu kayayyakin ma sun nunka farashin har sau uku saboda gaza ɗakko su daga Ukraine da wasu sassan duniya, hakan ya shafi masana'antu."
"Dan haka a ayyuka an saka wannan adadin (na yuwuwar tashin farashi) a kaso 5, amma yanzun abinda muke fuskanta ayyukan na bukatar kashi 25 domin cigaba."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Majalisar Shugabannin Ƙasa sun sanya ranar ƙidaya yawan Yan Najeriya

A ɓangarensa, shugaban sashin binciken iingancin ayyuka (NIQS), Mr Olayemi Shonubi, ya ce akwai bukatar yin garambawul kan kasafin kudin shekarar 2022 domin ya yi dai-dai da halin da ake ciki.

Shonubi ya ce:

"Ta ya zamu jawo hankalin gwamnati ta kawo mana tsarin kasafin kuɗin ta yadda zamu samu saukin ayyukan mu. Ba wanda ya san Rasha zata afka wa Ukraine, kuma mun san cewa ta mana illa a masana'antun mu."
"Game da kayayaki a duniya, farashin dakon su ya tashi sosai, farashin jigilar kaya ya yi tashin gwauron zabi, ta ya abokanan cinikin mu zasu fahinta."

A wani labarin kuma Jarumin Kannywood Lukman na Shirin Labarina ya fito takarar siyasa a jihar Kano

Yayin da zaɓen 2023 ke ƙara ƙaratowa, yan Najeriya dake da niyyar tsayawa takara na cigaba da faɗa wa duniya aniyarsu.

A masana'antar Kannywood, Jarumi Lukman na Labari na ya bayyana tsayawa takarar ɗan majalisar tarayya daga Kano.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun harbe Fitaccen ɗan kasuwa har Lahira a gaban Budurwar da zai Aura mako mai zuwa

Asali: Legit.ng

Online view pixel