Abinda shugaba Buhari ya faɗa wa Gwamnan APC bayan sanar da shi aniyarsa ta takara a 2023
- Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya sanar da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari aniyarsa ta tsayawa takara a 2023
- Wata majiya ta bayyana cewa shugbaan ya ƙarfafa wa gwamnan guiwa ya cigaba da kokarin cika burinsa
- Gwamna Fayemi, shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ya ce har yanzun bai kammala shawari kan aniyarsa ba
Abuja - Bayanai sun nuna cewa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ƙara wa gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, kwarin guiwa kan cigaba da kokarin cika burinsa na zama shugaban ƙasa.
Premium times ta rahoto wata majiya a fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa gwamnan ya samu kyakkyawan tarba lokacin da ya ziyarci Aso Villa domin sanar da Buhari niyyar tsayawa takara karkashin APC.
Majiyar ta ce:
"Shugaban ƙasa ya tarbe shi da kyau, kuma ya ba shi kwarin guiwar kada ya gajiya, inda ya ce a iya aikin da suka yi tare na yan shekaru, yana da yaƙinin zai zama magaji na kwarai."
A cewar majiyar, babu tabbacin ko Buhari zai nuna goyon baya ga gwamna Fayemi, musamman saboda har yau bai fito da abinda ke zuciyarsa ba game da wanda yake so ya gaje shi.
A ranar Talata da daddare, gwamna Fayemi ya tabbatar da cewa ya gana da shugaban ƙasa Buhari, amma ya kauce wa yin ƙarin bayani kan tattaunawar su.
Har yanzun ina neman shawara ne - Fayemi
Shugaban ƙungiyar gwamnoni ta ƙasa NGF, Kayode Fayemi, ya ce har yanzun yana cigaba da neman shawari ne kan burinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa.
Legit.ng ta tattaro cewa gwamnan ya bayyana haka ne a Gombe yayin wata ziyara da ya kai wa takwaransa na jihar, Gwamna Inuwa Yahaya.
Yace wannan lokaci ne mai tsada a wurin yan Najeriya, dan haka yan Jarida su jira mutane su kammala ibadun su kafin jin ta bakinsa.
Idan ban gyara Najeriya a shekara ɗaya ba ku mun kiranye, Ɗan takarar shugaban ƙasa ya roki dama a 2023
A wani labarin kuma Ɗan takarar shugaban ƙasa a PDP ya ɗauki alƙawarin gyara Najeriya a shekararsa ta farko bayan zama shugaban ƙasa a 2023
Ɗan takarar shugaban ƙasa a PDP ya lashi takobin kawo sauyi a Najeriya cikin shekara ɗaya da zaran yan Najeriya sun ba shi dama.
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Pius Anyim, ya ce idan bai gyara Najeriya a wannan lokacin ba a masa kiranye.
Asali: Legit.ng