Gwamna Fayemi ya gana da shugaba Buhari kan aniyarsa ta takarar shugaban ƙasa a 2023

Gwamna Fayemi ya gana da shugaba Buhari kan aniyarsa ta takarar shugaban ƙasa a 2023

  • Shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi, ya gana da Buhari kan niyyarsa ta neman shugaban ƙasa a 2023
  • Gwamnan ya sanar da shugaban ƙasa aniyarsa kuma Buhari ya ƙara masa kwarin guiwa da sanya masa albarka
  • Wata majiya ta ce gwamnan bai ayyana lamarin a hukumance bane saboda darajar watan Ramadan

Abuja - Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya sanar da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, aniyarsa ta neman tikitin takarar shugaban ƙasa a APC.

Wata majiya daga Aso Villa ta shaida wa jaridar Premium Times cewa gwamnan ya shaida wa Buhari niyyarsa tun kafin zaɓen fidda ɗan takara.

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari da Gwamna Kayode Fayemi.
Gwamna Fayemi ya gana da shugaba Buhari kan aniyarsa ta takarar shugaban ƙasa a 2023 Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Jami'in gidan gwamnatin ƙasa wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi da hurumin zanta wa da yan jarida kan lamarin, ya ce:

"Ya zo nan fadar shugaban ƙasa mako biyu da suka shuɗe ya sanar da shugaba Buhari niyyarsa ta shiga tseren."

Kara karanta wannan

Idan ban gyara Najeriya a shekara ɗaya ba ku mun kiranye, Ɗan takarar shugaban ƙasa ya roki dama a 2023

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Shugaban ƙasa ya karɓe shi hannu biyu-biyu ya kuma ƙara masa kwarin guiwar ya nema, inda ya faɗa masa cewa kasancewar ya yi aiki da shi na shekaru, ya na da kwarin guiwar zai zama magaji na kwarai."

Majiyar ta ƙara da cewa babu tabbacin ko shugaba Buhari zai yi amanna ya goyi bayan takarar Fayemi, musamman kasancewar ya ɓoye wanda yake son ya gaje shi.

Yayin da aka tuntuɓi gwamna Fayemi, ya tabbatar da cewa ya tattauna da shugaba Buhari, amma ya guje wa faɗin abin da ya kai shi.

Buhari da Fayemi na da kyakkyawar alaƙar siyasa kusan shekara 10 wacce ta fara a 2012 lokacin da jam'iyyun hamayya suka yi maja wuri ɗaya.

Bayan Shugaba Buhari ya ci zaɓe a 2015, ya naɗa Kayode Fayemi a matsayin minista, muƙamin da ya rike har zuwa 30 ga watan Mayu, 2018, lokacin da ya aje aikin domin ya sake neman gwamnan Ekiti.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC da Sanata sun sanar da Buhari zasu shiga takarar shugaban ƙasa a 2023

Meyasa bai ayyana niyyarsa ga duniya ba?

Wata majiya ta kusa da Fayemi ta ce har yanzun gwamnan na sha'awar takarar shugaban ƙasa a APC, amma ya jinkirta zuwa lokacin da ya fi dacewa ya ayyana a hukumance.

Ya ce:

"Kamar yadda kuka sani wannan lokaci ne mai Daraja a wurin Musulamai da Kiristoci. Gwamna na ganin bai dace ba a kawo wata harkar siyasa a irin lokacin. Amma tabbas zai bayyana niyyarsa da zaran Ramadan ya ƙare."

A wani labarin kuma Bayan Sanata Adamu, wani babban Jigon APC ya yi murabus daga muƙaminsa

Donald Ojogo, ya miƙa takardar murabus ɗinsa daga gwamnatin gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ba tare da jinkiri ba.

Gwamna Akeredolu, idan ba ku manta ba ya ba hadimansa dake niyyar takarar siyasa awanni 48 su aje muƙamansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel