2023: Idan Jonathan yace zai yi takara zan janye, Kauran Bauchi
- Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan bai gama yanke shawara ba kan tsayawa takarar shugaban kasa a 2023
- Mohammed ya ce ba zai shiga tseren ba idan har tsohon shugaban kasar zai yi takarar shugabancin kasar a zaben 2023
- Jigon na jam’iyyar PDP ya bayyana cewa ya shigo ana damawa da shi harkar siyasa ne ta sanadiyar tsohon shugaban kasar
Abuja - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan bai gama yanke shawarar ko zai yi takarar shugabancin kasar ba a 2023.
Mohammed ya bayyana hakan ne a daren ranar Talata, 12 ga watan Afrilu, yayin ganawarsa da kungiyar tsoffin ministocin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), rahoton Nigerian Tribune.
Ya bayyana cewa da ace tsohon shugaban kasar zai yi takarar kujerar a zaben 2023, toh da ba zai taba shiga tseren ba.
Rahoton ya nakalto Mohammed yana fada ma kungiyar tsoffin ministocin cewa:
“Na tuna na fada ma duniya cewa idan ubangidana, Shugaba Jonathan zai yi takara, ni ba zan yi takara ba, ba wai don ban kai ba sai don biyayya.
“Na shigo ana damawa dani ne a matakin kasa ta sanadiyarsa. Kuma na yarda cewa ya yi kokari sosai. Kuma ina fadi a kowani yanki saboda koda zai yi takara ne a APGA ko ma a ina ne, b azan yi takara ba saboda ba zan sa kafar wando daya da shi ba.
“Shakka babu, ni dan PDP ne, b azan je koina ba. Don haka har zuwa yanzu, bai yanke shawara ba. Lokaci ya yi da zan fito, wannan ne dalilin da yasa na fara da ku.”
Bala Mohammed: Buhari ya yi rugu-rugu da Najeriya amma ni zan gyara ta
A wani labarin, Gwamnan jihar Bauchi kuma mai aniyar son zama shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Bala Mohammed ya caccaki jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Da yake magana a daren ranar Talata, 12 ga watan Afrilu, a wajen wani taro da tsoffin ministocin gwamnatin PDP suka shirya, Mohammed ya bayyana cewa jam’iyyar mai mulki ta lalata komai da komai na kasar, The Cable ta rahoto.
Mohammed ya bayyana gwamnatin Buhari a matsayin mai nuna son kai, inda ya kara da cewa idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa zai gudanar da gwamnati mai yi da kowa.
Asali: Legit.ng