Da duminsa: Dattawan Arewa sun bukaci murabus din Buhari, sun sanar da dalilinsu

Da duminsa: Dattawan Arewa sun bukaci murabus din Buhari, sun sanar da dalilinsu

  • Kungiyar dattawan arewacin Najeriya ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi murabus da gaggawa
  • kamar yadda kakakin kungiyar NEF, Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya sanar, shugaba Buhari ya gaza bai wa rayuka da dukiyoyi tsaro
  • Ya sanar da cewa hatta 'yan Najeriya za su murna idan Buhari ya karba shawarar nan saboda ba za a iya jira har wa'adin mulkinsa ya kare a 2023 ba

Kungiyar Dattawan Arewa (NEF), ta bukaci murabus din shugaban kasa Muhammadu Buhari nan take sakamakon yawaitar kashe-kashe a fadin kasar nan ballantana arewaci.

Daily Trust ta ruwaito cewa, daraktan yada labaran kungiyar, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya yi wannan kiran a ranar Talata.

Da duminsa: Dattawan Arewa sun bukaci murabus din shugaba Buhari da gaggawa
Da duminsa: Dattawan Arewa sun bukaci murabus din shugaba Buhari da gaggawa
Asali: Original
"Mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari bai magance kalubalen tsaro da muke ciki ba. Ba za mu cigaba da rayuwa tare da mutuwa a karkashin makasa, masu garkuwa da mutane, masu fyade da sauran kungiyoyin ta'addanci da suke hana mu hakkinmu na zaman lafiya da tsaro ba.

Kara karanta wannan

Hotuna: Kaakin majalisar wakilai, dimbin yan majalisa sun dira birnin Madina aikin Umrah

"Kundin tsarin mulkinmu ya bukaci shugabanni su sauka daga mulki idan suna fama da wani kalubale na kansu ko kuma sun kasa shugabancin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A yanzu lokaci ya yi da shugaba Buhari zai dauka wannan zabin tunda a bayyane yake shugabancinsa ya gaza samar da tsaro ga 'yan Najeriya. Kungiyar mu ta san nauyin wannan shawarar kuma ta san ba za mu iya cigaba da rayuwa a irin wannan halin ba har 2023 lokacin da wa'adin mulkin Buhari zai kare," Baba-Ahmed yace.

Ya ce kungiyar ta mika wannan bukatar ne kuma tana fatan 'yan Najeriya masu tarin yawa za su ji dadin hakan idan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbeta.

Ya jajanta kashe-kashe da cin zarafin da ake wa yankuna wanda ya zama ruwan dare kuma a kowacce rana ga 'yan Najeriya. A halin yanzu tafiya ta zama babban hatsari kuma zaman wuri dayan haka yake.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da motoci biyu na matafiya a jihar Ribas

Ya ce, "Makasa da sauran 'yan ta'adda sun shinshino nakasa kololuwar shugabanci kuma suna cigaba da kamari tare da samun karin kwarin guiwa wurin addabar kasar mu da tsaronmu.
"Yan Najeriya sun zubda hawaye iyakar iyawarsu da jini wanda har yanzu wadanda ke da alhakin daukan matakin bamu kariya sun gaza."

Independent.ng ta ruwaito cewa, ya shawarci 'yan siyasa da ke son mulkar kasar nan da su duba nauyin hakkin da kuma kalubalen shugabanci da kyau.

A Tsige Buhari Idan Bai Zai Iya Samar Da Tsaro Ba, Hakeem Baba-Ahmad

A wani labari na daban, Mai magana da yawun kungiyar dattijan Arewa (NEF), Hakeem Baba-Ahmed, ya bukaci majalisa da ta tsige shugaba Muhammadu Buhari idan ba zai iya samar da tsaro ga yan kasa ba, rahoton Daily Trust.

Shugaban na fuskantar matukar matsin lamba sakamakon karuwar rashin tsaro a kasar nan.

Da yake magana a shirin Kakaaki, na gidan talabijin din AIT, ranar Litinin, Baba-Ahmed ya bukaci masu rike da mukamai da su fahimci halin da kasar nan ke ciki, su kuma yi wani abu na daukar mataki ba wai daukar alkawarurruka ba.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta gurfanar da Janar din Sojan Bogi kan damfarar miliyoyi

Asali: Legit.ng

Online view pixel