Yahaya Bello: Ƙaruwar Masu Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa Baya Bani Tsoro Ko Kaɗan

Yahaya Bello: Ƙaruwar Masu Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa Baya Bani Tsoro Ko Kaɗan

  • Gwamnan Jihar Kogi kuma dan takarar shugaban kasar Najeriya a APC, Yahaya Bello, ya ce bai tsorata ba da yadda masu fitowa takarar shugaban kasa suke kara yawa ba
  • A cewarsa ba ya fargabar shirye-shiren yarjejeniyar da ake yi kuma yana da yakinin kasancewa mai nasara komai rintsin yadda aka shirya zaben dan takarar jam’iyyar APC
  • Bello ya yi wadannan furucin ne a wani taron manema labarai a Abuja wanda Kungiyar Kamfen din shugabancin kasar Yahaya Bello ta shirya

Abuja - Dan takarar shugaban kasa kuma Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce ko fargaba ba ya yi akan yadda mutane da dama suke ta fitowa takarar shugaban kasa, The Punch ta ruwaito.

Haka zalika, ya ce bai tsorata ba da shirye-shiryen yarjejeniyar jam’iyya ba saboda yana sa ran kasancewa mai nasara a ko wanne irin mataki jam’iyyar ta dauka wurin zaben dan takara.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Bayan ganawa da gwamnoni, Osinbajo ya gayyaci 'yan majalisun APC

Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da Kungiyar Kamfen din shugabancin kasar Yahaya Bello ta shirya a Abuja.

Yahaya Bello: Ƙaruwa Masu Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa Baya Bani Tsoro
'Karuwa Masu Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa Baya Razana Ni, Yahaya Bello. Hoto: The Nation.
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan furucin nasa ya biyo bayan kwana daya da Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana kudirinsa na tsayawa takara da kuma jagoran APC, Bola Tinubu, wanda ya nemi goyon bayan gwamnonin APC akan shirinsa na tsayawa takara.

Ya ce bai razana da irin gogewar masu tsayawa takarar ba

Gwamnan wanda ya samu wakilcin kwamishinan labaransa, Kingsley Fanwo kamar yadda Vanguard ta nuna, ya kada baki ya ce:

“Ban razana da irin gogewa da kuma irin hidimar da suka yi a baya ba. Sai dai ka kwatanta da abin da mutum yake yi yanzu, ina tunanin su ne ya kamata su razana a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Manyan jihohin kudu maso yamma 3 da Osinbajo zai iya rasawa idan ya zama dan takarar APC

“Gwamnan ya samu gogewa kuma shekaru 6 zuwa 7 kenan da ya ke mulkar jiharsa. Muna da tabbacin zai yi wa Najeriya aiki na gani da fadi.”

Ya ce za a tsayar da dan takaran da ya cancanta ne daga ko wanne bangare

Ya ci gaba da cewa zai yanko maganar da gwamnan ya yi:

“Gwamnan ya ce an haife shi a Arewa ta Tsakiya. An haife shi a dan kabilar Egbira. Ba ni na zabi zama Egbira ba. Ban zabi zama dan arewa ba. Don haka bangaranci bai dace ya dakatar da mutum daga takara ba.
“Muna yawan kawo hakan a siyasa. Amma ba ma kawo batun a wuraren aiki. Yanzu direban da zai kai ka Onitsha daga nan, me ne ne burinka akan shi? Ba kawai sanin idan direban kwarai bane?
“A siyasa ana tambayar daga wanne yanki mutum yake? A shekarar 2023 lamarin zai sauya. Za a zabi wanda ya fi cancanta, jajircewa da kuma wanda zai gina kasa ne kawai. Babu wani batun dan kudu, arewa, Ibo ko Bahaushe.”

Kara karanta wannan

Zan daura daga inda Buhari ya tsaya: Alkawura 10 na Osinbajo idan ya zama shugaba a 2023

Ya bayyana dalilin gwamanan na bayyana kudirinsa a Abuja

An tambaye shi dalilin da ya sa gwamnan ya bayyana kudirinsa a babban birnin tarayya maimakon jiharsa kamar yadda sauran ‘yan takara suka yi, Fanwo ya ce FCT ta kowa ce don haka nan ne ya fi dacewa.

Ya ci gaba da cewa Bello yana son zama shugaban kasar Najeriya ne ba shugaban Jihar Kogi ba. Kuma a tsakiyar kasa ya dace mutum ya yi kira ga mutanensa ba a wani yanki ba.

2023: Zan iya shugabancin Najeriya amma dai ban matsu ba, Orji Kalu

A wani labarin, bulaliyar Majalisar Dattawa, Orji Uzor Kalu, ya ce duk da a shirye ya ke da ya yi kamfen kuma zai iya shugabantar kasar nan, amma bai matse ya ce ai zama shugaban Najeriya ba, Daily Trust ta ruwaito.

Kalu, tsohon gwamnan Jihar Abia, ya yi wannan bayanin ne a ranar Laraba yayin amsa tambayoyi daga manema labarai a Majalisar Tarayya, washegarin da ya kai wa Buhari ziyara a fadarsa da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164