Wani Gwamna ya sake ba Mukarrabansa daga nan zuwa Ranar Juma’a su ajiye mukamansu

Wani Gwamna ya sake ba Mukarrabansa daga nan zuwa Ranar Juma’a su ajiye mukamansu

  • Mai girma Gwamnan jihar Kwara ya bukaci duk wanda zai shiga takara ya ajiye masa mukaminsa
  • AbdulRahman AbdulRazaq ya fitar da sanarwa ta bakin Sakataren Gwamnatin Kwara a kan batun
  • Dokar zabe ta tursasawa duk wanda aka ba mukami barin kujerarsa kafin shiga zaben fitar da gwani

Kwara - Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya umarci masu neman yin takara a zaben 2023 da ke gwamnatinsa, da su ajiye mukamansu.

Punch ta ce wannan sanarwa ta fito ne daga bakin Sakataren gwamnatin jihar Kwara, Farfesa Mamman Jibril a ranar Talata, 12 ga watan Afrilu 2022.

A takardar da SSG, Farfesa Mamman Jibril ya sa wa hannu, an bukaci wadanda gwamna ya ba mukami da ke harin takara, su rubuta takardar yin murabus.

Dole ne duk wani hadimin gwamnan na Kwara ya ajiye aikinsa kafin ranar Juma’a, 15 ga watan Afrilu 2022, kamar yadda sabuwar dokar zabe ta yi tanadi.

Kara karanta wannan

Karin Bayani da Hotuna: Tinubu ya sa labule da gwamnonin APC jim kaɗan bayan Osinbajo ya shiga takarar 2023

Haka dokar zabe ta ce - SSG

AbdulRahman AbdulRazaq ya ce dokar zabe ta shekarar 2022 da Muhammadu Buhari ya rattabawa hannu ta bukaci mukarrabai su sauka kafin zabe.

Gwamnan yake cewa za a gabatar da duk wata takardar ajiye aiki ne ga ofishin sakataren gwamnatin jihar Kwara daga yanzu zuwa ranar Juma’ar nan.

Gwamnan Kwara
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

An yi wa takarda take da ‘RESIGNATION OF APPOINTEES SEEKING ELECTIVE POSITIONS’, ma’ana murabus din mukarraban da ke shirin neman takara.

Hadiman Gwamna za su yi takara

Tribune ta ce daga cikin wadanda ke rike da mukamai a gwamnatin AbdulRahman AbdulRazaq, akwai masu manufar yin takara a zaben shekara mai zuwa.

Mai ba gwamna shawara a kan harkar tsaro, Yinka Aluko zai nemi kujerar Sanatan Kwara ta tsakiya. Bukola Saraki ya rike wannan kujera har zuwa 2019.

Kara karanta wannan

Bauchi: An Kama Mai Hidimar Ƙasa Na Bogi Ya Saci Wayoyi a Sansanin NYSC

Sannan Kwamred Musbau Esinrogunjo wanda shi ne mai ba gwamna shawara a kan harkar wayar da kan mutanen karkara, ya na cikin masu niyyar takara.

Akwai irinsu Ambasada Yahaya Seriki, Hajia Saadat Modibbo Kawu da suka ayyana shirin neman kujerar majalisar wakilai da na dattawa a zaben 2023.

Ku ajiye aiki idan za ku yi takara a Ondo

A jiya aka ji labari Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya bada umarnin murabus na gaggawa ga duk wani hadiminsa dake hangen wata kujerar siyasa.

Gwamnan ya ce matakin da ya ɗauka ya yi dai-dai da tanade-tanaden dokokin zaɓe. Akeredolu ya ce ya zama dole su bi dokar Najeriya, duk da dai maganar ta na kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng