Gwamnan APC ya umarci wasu kwamishinoni da hadimansa su yi murabus cikin awanni 48

Gwamnan APC ya umarci wasu kwamishinoni da hadimansa su yi murabus cikin awanni 48

  • Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya ba da umarnin murabus ɗin gaggawa ga duk wani hadiminsa dake hangen wata kujera a 2023
  • Akeredolu ya ɗauki wannan matakin ne a wata takarda mai ɗauke da ranar 11 ga watan Afrilu kuma Sakataren gwamnati ta rattaɓa hannu
  • Gwamnan ya ce matakin da ya ɗauka ya yi dai-dai da tanade-tanaden dokokin zaɓe kuma tilas mambobin majalisarsa su yi ɗa'a

Ondo - Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, a ranar Talata 12 ga watan Afrilu, 2022 ya ba da umarnin gaggawa ga masu hangen kujerun siyasa a 2023.

Gwamnan ya umarci duk wasu masu rike da naɗin siyasa da kuma Ofisoshin gwamnati wadan ke hange da sha'awar neman takara a kowane mataki su yi murabus kafin Alhamis mai zuwa.

Gwamna Rotimi Akeredolu.
Gwamnan APC ya umarci wasu kwamishinoni da hadimansa su yi murabus cikin awanni 48 Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Umarnin gwamnan na kunshe ne a wata takarda mai ɗauke da kwanan watan Litinin 11 ga watan Afrilu, 2022 kuma Sakatariyar gwamnatin jiha, Princess Oladunni Odu, ta rattaba hannu.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Mataimakin shugaban ƙasa zai yi buɗe bakin Azumi da Sanatocin Jam'iyyar APC

PM News ta rahoto gwamnan na cewa duk waɗan da wannan umarnin ya shafa, ana umartan su da su miƙa takardar aje aiki ranar ko kafin Alhamis 14 ga watan Afrilu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani sashin umarnin gwamnan ya ce:

"Bisa tanadin sashe na 84 (12) na kundin dokokin zaɓe 2022, masu rike da muƙaman siyasa da ofishin gwamnati waɗan da ke son shiga harkokin zaɓe, ya Allah takara ko Deleget su yi murabus a ranar ko kafin 14 ga watan Afrilu."
"Mun yi haka ne domin ankarar da ku ko Allah zai sa ku yi biyayya."

Su wa abun zai shafa a gwamnatin Ondo?

Akwai kwamishinoni da wasu hadiman gwamnan da suka nuna sha'awar neman takarar kujerar siyasa tsakanin majalisar dokokin jiha zuwa ta dattawa. kamar yadda Daily Independent ta rahoto.

Idan dukan kwamishinoni da hadiman gwamnati da abun ya shafa zasu aje muƙamansu kafin Alhamis, hakan zai ba gwamnan damar sake ɗakko ƴaƴan APC ya naɗa a gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu, Amaechi da wasu jiga-jigan APC 4 da Osinbajo zai gwabza da su ya gaji Buhari

A wani labarin kuma Gwamnan APC da Sanata zasu ayyana takarar shugaban ƙasa, sun sanar da Buhari

Jiga-Jigan siyasa musamman masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC sun shirya shiga tseren takarar shugaban ƙasa a 2023.

Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti da Sanata Ibikunle Amosun na shirin sanar da shirinsu na neman kujera lamba ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel