Sai dai ka ga wasu suna yi: Babban fasto ya ce Osinbajo ba zai taba zama shugaban kasa ba

Sai dai ka ga wasu suna yi: Babban fasto ya ce Osinbajo ba zai taba zama shugaban kasa ba

  • Babban limamin coci, Primate Elijah Ayodele, ya gargadi mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo kan kudirinsa na son zama shugaban kasa
  • Ayodele ya shawarci Osinbajo da kada ya barnatar da kudinsa domin ba zai taba zama shugaban kasar Najeriya ba
  • Faston ya ce akwai wasu tawaga da za su hade masa kai sannan kuma su yi masa bita da kulli idan har ya dage sai ya yi takarar kujerar Buhari

Babban faston Najeriya, Primate Elijah Ayodele, ya fada ma mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo wanda ya ayyana kudirinsa na son takarar shugaban kasa a 2023 cewa yana bata lokacinsa ne domin ba zai taba nasara ba.

Malamin addinin wanda ya kasance shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, ya gargadi Osinbajo kan kudirin nasa a ranar Talata, 12 ga watan Afrilu, New telegraph ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yadda na zama mataimakin shugaban kasa, Osinbajo ya bada labari mai taba zuciya a bidiyo

Primate Ayodele ya yabawa mataimakin shugaban kasar kan ayyana kudirinsa da ya yi, amma ya bayyana cewa ba zai taba zama shugaban kasar Najeriya ba.

Sai dai ka ga wasu suna yi: Babban fasto ya ce Osinbajo ba zai taba zama shugaban kasa ba
Sai dai ka ga wasu suna yi: Babban fasto ya ce Osinbajo ba zai taba zama shugaban kasa ba Hoto: Yemi Osinbajo
Asali: Facebook

A wani jawabi dauke da sa hannun hadimin labaransa, , Osho Oluwatosin, Primate Ayodele ya yi gargadin cewa ci gaba da wannan yunkuri na son cimma kudirin zai haifar da barnar dukiya saboda wasu tawaga za su yake shi sannan su yi masa bita da kulli.

Daily Post ta nakalto Ayodele yana cewa:

“Abu mai kyau ne cewa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ayyana kudirinsa na son zama shugaban kasa domin zuciyarsa ta samu nutsuwa, amma ba zai taba zama shugaban kasar Najeriya ba, ayyana kudirinsa tamkar kawai mutum ya fitar da abun da ke damunsa ne a zuciya.

Kara karanta wannan

Manyan jihohin kudu maso yamma 3 da Osinbajo zai iya rasawa idan ya zama dan takarar APC

“Imma dai ya barnatar da kudinsa ko kuma ya yanke shawarar adana kudinsa, amma dai ba zai taba zama shugaban kasar Najeriya na gaba ba. Za su yi masa bita da kulli, yan arewa basa son sa kuma wasu za su yi adawa da shi, ba zai taba kaiwa wajen ba.
“Babu aibu a ciki don mutum ya bayyana kudirinsa, amma Osinbajo ba zai taba nasara ba, cin amana ko akasin haka, Allah baya fushi da kudirin Osinbajo, amma zai barnatar da kudi saboda bai bi hanyar daidai ba.
“Za a tuhume shi, wannan ayyanawar na tarihi ne kawai, ba zai kai koina ba. Suna yaudararshi ne, ba zai je sama da mataimakin shugaban kasa ba, kada ya barnatar da kudinsa ko kadan.”

Manyan jihohin kudu maso yamma 3 da Osinbajo zai iya rasawa idan ya zama dan takarar APC

A wani labarin, mun ji cewa cece-kuce ya biyo bayan ayyana kudirin son gaje Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya yi.

Kara karanta wannan

2023: Amaechi ya fara neman shawarwari, ya ziyarci sarakunan Daura, Kano da Bichi

Hakan ya nuna za a kai ruwa rana a yayin zaben fidda gwani na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a inda za ta zabi dan takararta na shugaban kasa.

Ayyana neman takarar Osinbajo na nufin sa kafar wando daya da tsohon ubangidansa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wanda ya kwallafa rai a kan son zama shugaban kasar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng