Jam'iyyar PDP ta lallasa APC, ta lashe zaben Ciyamomi 21 da Kansiloli 226 a jihar Adamawa

Jam'iyyar PDP ta lallasa APC, ta lashe zaben Ciyamomi 21 da Kansiloli 226 a jihar Adamawa

  • Jam'iyyar PDP mai mulkin jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya ta cigaba da jan zarenta a zaɓen kananan hukumomi
  • Jam'iyya mai mulki ta lallasa abokiyar hamayyarta APC, ta lashe dukkan kujerun Ciyamomi 21 da kuma Kansiloli 226
  • APC ta yi watsi da sakamakon zaben da cewa ba'a gudanar da zaɓe ba, wasu ne kawai suka rubuta abinda ke ransu

Adamawa - Jam'iyyar PDP ta lashe baki ɗaya kujerun Ciyamomi da Kansiloli a faɗin kananan hukumomi 21 na jihar, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Jam'iyyun siyasa da ba su gaza 18 ba ne suka tsayar da yan takara a zaɓen kananan hukumomin wanda aka gudanar ranar Asabar.

Da yake sanar da sakamakon zaɓen ranar Lahadi a Yola, babban birnin jihar Adamawa, shugaban hukumar zaɓen jiha mai zaman kanta (ADSIEC), Mr. Isa Shettima, ya ce APC da PDP ne kawai suka ɓarje gumi a zaɓen ciyamomi.

Jam'iyyar PDP ta lallasa APC a Adamawa
Jam'iyyar PDP ta lallasa APC, ta lashe zaben Ciyamomi 21 da Kansiloli 226 a jihar Adamawa Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Shettima ya ce:

"Daga cikin jam'iyyu 18 da suka nuna sha'awa, Jam'iyyar PDP da APC ne kawai suka gwabza a zaɓen shugabannin kananan hukumomi."

Ya APC ta ji wannan shan ƙasa da ta yi?

Kakakin APC-Adamawa, Abdullahi Mohammed, da aka tuntuɓe shi, ya bayyana cewa babu wani zaɓen da aka gudanar a jihar, domin ba'a kai kayan zabe wasu runfuna na ba sam.

Ya ce a APC na cigaba da tattara kwararan shedun aikata maguɗi a zaɓen kuma zata sanar da matsayarta ba da jimawa ba, kamar yadda The cable ta rahoto.

Ya ce:

"Ba wani zaɓe da aka gudanar a baki ɗaya yankunan kananan hukumomi 21 dake faɗin jihar. Wasu tsirarun jami'an gwamnati ne suka zauna suka tsara sakamakon da ransu ke so."

"APC ba zata yi ƙasa a guiwa ba, zata cigaba da harhaɗa kwararan shedu, ba da jimawa ba kowa zai ji matsayarta."

A wani labarin kuma Hotunan Katafariyar Gada Mai Hawa Uku da Ganduje Ke Ginawa a Kano, Babu Irinta a Faɗin Najeriya

Gwamnatin Kano na cigaba da aikin gada mai hawa uku a Shataletalen NNPC dake Anguwar Hotoro.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce suna sa ran kammala aikin zuwa watan Satumba, an raɗa wa Gadar 'Muhammadu Buhari Interchange.'

Asali: Legit.ng

Online view pixel