Masu fasa bututu sun taso Najeriya a gaba, ana asarar Naira Biliyan 600 a kowace rana

Masu fasa bututu sun taso Najeriya a gaba, ana asarar Naira Biliyan 600 a kowace rana

  • Shugaban kamfanin man NNPC, Mele Kolo Kyari ya bayyana a gaban majalisar wakilan tarayya
  • Mele Kolo Kyari ya yi tir da aikin masu fasa bututun danyen mai da masu matatan da ba su da rajista
  • Wannan matsala ta jawo ake tunanin gwamnatin tarayya ta yi asarar $1.5bn a cikin farkon 2022

Abuja - Shugaban kamfanin mai na kasa watau NNPC, Mele Kolo Kyari ya koka a game da yadda ‘yan fasa kauri suke cin karensu babu babbaka a yau.

Daily Trust ta rahoto Mele Kolo Kyari ya na cewa ana samun matsaloli a dalilin dayen aikin masu fasa bututu da kuma masu matatan da ba a san da su ba.

Mele Kyari ya yi wannan bayani ne a sa’ilin da ya bayyana a gaban kwamitin harkar mai na majalisar wakilan tarayya a ranar Talatar da ta gabata.

Shugaban kafmfanin NNPC ya shaidawa ‘yan majalisa cewa aikin mabarnatan ya jawo an rasa danyen man Dala biliyan 1.5 daga Junairu zuwa yau.

A cewar Kyari, tattalin arzikin kasa ya yi baya a sanadiyyar karancin man da ake hakowa saboda masu fasa bututu, su na barna a yankin Neja-Delta.

A halin yanzu, gangunan danyen man da Najeriya ta ke fitarwa a kullum bai wuce miliyan 1.49 ba. Ya kamata a ce adadin gangunan ya zarce haka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Layin man NNPC
Wani layin mai Hoto: businesspost.ng
Asali: Facebook

“Abin da ke faruwa bai da alaka da dokar PIA. Zallar aikin wasu barayi ne; masu fasa bututu sun nakasa harkar hako danyen mai.”
“Sun jefa mu a wani mawuyacin hali, sun kai mu cikin yanayin da mu ka samu kanmu. Ganguna miliyan 1.9 muke hakowa kullum.”
“Idan ka yi asarar ganguna 200, 000 a duk rana, ko da an yi lissafin farashin ganga a $65 ne, mun rasa kusan $1bn daga Junairu zuwa Maris.”

“Mun yi asarar kimanin ganguna 250, 000 ne a duk rana, kuma farashin mai a kasuwa yau ya kai $100, kenan har mun rasa kusan $1.5bn

An rahoto Kyari ya na fadawa ‘yan majalisa cewa abin ya yi muni a farkon Maris na 2022, inda ba a iya samun ko sisi daga kudin danyen man kasar ba.

Dokubo Asari v Nyesom Wike

An ji Alhaji Mujaheed Dokubo-Asari ya ce bai ganin cewa Gwamna Nyesom Wike ya dace ya rike Najeriya. Asari ya bayyana wannan ne da aka yi hira da shi.

Mujaheed Dokubo-Asari wanda ya taba jagorantar kungiyar tsagerun Niger Delta Peoples Volunteer Force na kasa, ya caccaki Wike da kuma Peter Obi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel