Da Dumi-Dumi: Ministan Sufuri, Amaechi, ya bayyana sha'awar gaje Buhari a 2023
- Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana aniyarsa ta gaje Buhari a zaɓen 2023 dake tafe karkashin APC
- Tsohon gwamnan jihar Ribas ya ayyana kudirinsa a ranar Asabar a Filin wasa na Adokiye Amiesimaka Stadium dake jihar Ribas
- Ministan ya kasance a gwamnati a muƙamai daban-daban tun bayan dawowar mulkin demokaraɗiyya a 1999
Rivers - Ministan sufuri na tarayyan Najeriya, Honorabul Rotimi Amaechi, ya ayyana shiga tseren takarar kujerar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Amaechi, wanda ya jima yana musanta raɗe-raɗin shiga takara, ya tabbatar da kudirinsa a hukumance ranar Asabar, 9 ga watan Afrilu, 2022.
Ministan ya rubuta a shafinsa na dandalin sada zumunta Facebook cewa:
"Na tsaya a nan gaba gare ku ne domin na bayyana manufa ta kuma na sanar muku da bukata ta aiki a matsayin shugaban ku na gaba."
Tarihin siyasar Amaechi
Amaechi ya kasance a cikin gwamnati a muƙaman siyasa daban-daban tun bayan dawowar mulkin demokaraɗiyya a shekarar 1999.
Ya rike kujerar shugaban majalisar dokokin jihar Ribas na tsawon zango biyu daga 1999-2007, bayan haka ya kwashe shekara 8 a kan kujerar gwamnan Ribas daga 2007-2015.
Haka nan kuma Mista Amaechi na ɗaya daga cikin tsirarun ministocin da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya zarce da su bayan lashe zaɓe a karo na biyu a 2019.
Babu tantama yana ɗaya daga cikin Ministocin wannan gwamnatin da suka taɓuka abun a yaba, kuma shi ne jagoran yaƙin neman zaɓen Buhari a 2015 da 2019.
Tsohon gwamnan ya zama na farko daga cikin yan majalisar gwamnatin Buhari da ya shiga tseren, wasu na sha'awa amma har yanzun ba su ayyana aniyarsu ba.
A wani labarin kuma bayan Tambuwal, Bala Muhammed da Wike, wani gwamnan PDP ayyana aniyar shiga takarar shugaban ƙasa a 2023
Gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel, ya amsa kiran yan Najeriya na neman takarar shugaban ƙasa a 2023.
Gwamnan ya ce ya karbi Fam ɗin da wata kungiyar kare hakkin ɗan Adam ta siya masa na sha'awar takara a PDP.
Asali: Legit.ng