Bidiyon Sanata Abdullahi Adamu yayin da ya isa fadar shugaban kasa domin ganawa da Buhari
- Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya isa fadar shugaban kasa domin saka labule da Shugaban kasa Muhammadu Buhari
- Sanata Adamu wanda wannan ne karo na farko da suke ganawa da shugaban kasar tun bayan da ya kama aiki a matsayin shugaban APC ya samu rakiyar Gwamna Mala Buni
- Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ne ya sanar da labarin ganawar tasu a wata sanarwa da ya saki a yau Alhamis, 7 ga watan Afrilu
Fadar shugaban kasa, Abuja - A yanzu haka, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga cikin wata ganawar sirri da shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Sanata Abdullahi Adamu.
Wannan shine karo na farko da Sanata Adamu ke ganawa da shugaban kasar tun bayan da ya kama aiki a matsayin shugaban jam’iyyar mai mulki na kasa a yan makonni da suka gabata.
Mai ba shugaban kasa shawara a shafukan sadarwa ta zamani, Bashir Ahmad ne ya sanar da batun ganawar tasu a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Twitter.
Sanata Adamu ya samu rakiyar Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe zuwa ganin shugaban kasar a fadar gwamnati da ke babbar birnin tarayya, Abuja.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya rubuta a shafin nasa:
“Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu wanda ya samu rakiyar wanda ya gada, Mai girma Gwamna Mai Mala Bunin a jihar Yobe sun isa fadar shugaban kasa domin ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, ganawarsu ta farko da shugaban kasar tun bayan da ya kama aiki a makonni da suka gabata.”
Gwamna Buni ya miƙa ragamar jam'iyyar APC hannun sabon shugaba na ƙasa
A gefe guda, mun kawo a baya cewa sabon shugaban jam'iyyar APC ta ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya karbi jagorancin jam'iyya ta ƙasa daga hannun shugaban riko.
Shugaban kwamitin rikon kwarya da shirya babban taro kuma gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya damƙa ragamar APC a hannun Adamu a hukumance.
Hakan ya kawo ƙarshen tsawon watanni 21 da Buni ya jagoranci APC tun bayan naɗa shi shugaban kwamitin riko.
Asali: Legit.ng