Yanzu-Yanzu: Tsohon Shugaba a Majalisar Tarayya Ya Fice Daga APC, Ya Shiga Wata Jam'iyyar

Yanzu-Yanzu: Tsohon Shugaba a Majalisar Tarayya Ya Fice Daga APC, Ya Shiga Wata Jam'iyyar

  • Jam'iyyar APC mai mulkin kasa, a ranar Alhamis 7 ga watan Afrilu ta yi rashin daya daga cikin jiga-jigan yayanta, Lasun Yussuf, ya koma Labour Party
  • Yussuf wanda ya yi bikin komawarsa jam'iyyar Labour Party a Osun a ranar Alhamis, tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin tarayya ne
  • Tsohon dan majalisar zai fafata tare da wasu yan takarar a ranar 16 ga watan Yuli a lokacin da za a gudanar da zaben gwamnan Jihar Osun

Osogbo, Osun - Rt Honorabul Lasun Yussuf, tsohon mataimakin kakakin majalisar dokoki na tarayya, a ranar Alhamis, 7 ga watan Afrilu, ya koma jam'iyyar Labour Party, LP, a hukumance.

Yussuf ya sanar da komawarsa jam'iyyar ta LP a fili a ranar Alhamis a Osogbo, babban birnin Jihar Osun, kamar yadda New Telegraph ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tsohon Minista Ya Dawo PDP Bayan Shekaru 8 a APGA, Zai Yi Takarar Gwamna a 2023

Yanzu-Yanzu: Tsohon Shugaba a Majalisar Tarayya Ya Fice Daga APC, Ya Shiga Wata Jam'iyyar
Tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya Ya Fice Daga APC, Ya Shiga Wata Jam'iyyar. (Photo: I Support Hon Lasun Yusuf)
Asali: Facebook

Yana sa ran zai yi takarar kujerar gwamna ne a jihar wacce za a yi zaben a ranar 16 ga watan Yuli.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon dan majalisar, a baya-bayan nan ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar All Progressives Congress, APC, mai mulkin kasa.

Hadimin El-Rufai Ya Koma Jam'iyyar PDP, Zai Yi Takarar Gwamna a 2023

Jimi Lawal, Mashawarci na muamman ga gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, kan habbaka saka hannun jari, ya shiga jam'iyyar PDP a Jihar Ogun., rahoton Daily Trust.

Lawal, wanda ya ziyarci sakatariyar PDP a Abeokuta, ranar Asabar, ya kuma ayyana niyarsa na yin takarar gwamna a zabe da ke tafe.

Ma'aikacin bankin da ya samu horaswa a Landan ya nemi kujerar gwamna a karkashin APC a zaben 2019, amma ya sha kaye hannun Gwamna Dapo Abiodun.

Kara karanta wannan

PDP da APC sun yi babban rashi: Tsohon Sanata, tsaffin yan majalisa, mambobi 10,000 sun koma NNPP

Tsohon Minista Ya Dawo PDP Bayan Shekaru 8 a APGA, Zai Yi Takarar Gwamna a 2023

A bangare guda, Tsohon ministan labarai, Labaran Maku, ya dawo jam'iyyar PDP, don fafatawa a takarar gwamnan Jihar Nasarawa da gwamna mai ci yanzu Abdullahi Sule a babban zaben 2023, rahoton The Punch.

Maku ya dawo jam'iyyar PDP bayan shafe shekaru takwas a APGA, inda ya rike mukamin sakataren jam'iyyar na kasa kafin ficewarsa.

Da ya ke magana a ranar Laraba a mazabarsa ta Wakama, karamar hukumar Nasarawa-Eggon a jihar, tsohon ministan ya ce ya koma PDP ne saboda magoya bayansa sun bukaci hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164