Tsohon Minista Ya Dawo PDP Bayan Shekaru 8 a APGA, Zai Yi Takarar Gwamna a 2023

Tsohon Minista Ya Dawo PDP Bayan Shekaru 8 a APGA, Zai Yi Takarar Gwamna a 2023

  • Labaran Maku, tsohon ministan Labarai ya fice daga jam'iyyar APGA ya koma tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP don yin takarar gwamna a 2023
  • Maku ya ce ya dawo jam'iyyar PDP ne saboda masu goyon bayansa sun bukaci ya aikata hakan kuma ya amsa
  • Ibrahim Hamza, Sakataren watsa labarai na PDP, Jihar Nasarawa, ya tarbi Maku yana mai kira ga sauran yan PDP da suka bar jam'iyyar su dawo

Nasarawa - Tsohon ministan labarai, Labaran Maku, ya dawo jam'iyyar PDP, don fafatawa a takarar gwamnan Jihar Nasarawa da gwamna mai ci yanzu Abdullahi Sule a babban zaben 2023, rahoton The Punch.

Maku ya dawo jam'iyyar PDP bayan shafe shekaru takwas a APGA, inda ya rike mukamin sakataren jam'iyyar na kasa kafin ficewarsa.

Tsohon Minista Ya Dawo PDP Bayan Shekaru 8 a APGA, Zai Yi Takarar Gwamna a 2023
Labaran Maku ya dawo PDP bayan shekaru 8 a APGA, Zai Yi Takarar Gwamna. Hoto: The Nation.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Abubakar Malami ya faɗi gaskiya kan rahoton shiga takara a zaɓen 2023

Da ya ke magana a ranar Laraba a mazabarsa ta Wakama, karamar hukumar Nasarawa-Eggon a jihar, tsohon ministan ya ce ya koma PDP ne saboda magoya bayansa sun bukaci hakan.

Sakataren watsa labarai na PDP, Jihar Nasarawa, Ibrahim Hamza, ya tabbatar da labarin, yana mai cewa ya yi farin cikin tarbar Maku kuma ya yi kira ga sauran yan jam'iyyar da suka fice su dawo don lema tana da girmar da za ta rufe dukkan mambobin jam'iyyar.

Ya ce:

"Muna murna da dawowar Maku PDP. Muna kuma kira ga wadanda suka bar jam'iyyarmu saboda wasu dalilai su dawo PDP don leman tana da girma da za ta ishe dukkan mambobin jam'iyyar.
"Muna aiki don tsayar da dan takara ta hanyar sulhu don babban zaben 2023 saboda kada mu samu matsala a jam'iyyar kuma hakan zai saukaka mana nasara kan jam'iyyar APC."

Maku, wanda ya fice daga PDP a 2015 bayan gaza samun tikitin takarar jam'iyyar, ya yi takara a 2015 da 2019 a APGA.

Kara karanta wannan

2023: Tambuwal da Peter Obi za su shiga labule da masu ruwa da tsaki na PDP a majalisar tarayya a yau

Ba A Ga Atiku Ba A Taron Da Wike Ya Yi Da Masu Neman Takarar Shugaban Ƙasa Na Jam'iyyar PDP

A bangare guda, kun ji cewa Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya bai halarci taron sirrn da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya shirya ba tare da wasu ‘yan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP ba, yayin da zaben fidda gwanin jam’iyyar ya ke karatowa.

An tattaro yadda ‘yan takarar suka dade suna tattaunawa dangane da wanda zai tsaya takara don gudun tashin tarzoma ta cikin jam’iyyar yayin zaben, The Nation ta ruwaito.

‘Yan takarar da suka halarci taron da aka yi gidan gwamnati da ke Port Harcourt sun hada da Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed; Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal; tsohon manajan darekta na bankin kasa da kasa na FSB, Dr. Mohammed Hayatu-Deen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel