PDP da APC sun yi babban rashi: Tsohon Sanata, tsaffin yan majalisa, mambobi 10,000 sun koma NNPP

PDP da APC sun yi babban rashi: Tsohon Sanata, tsaffin yan majalisa, mambobi 10,000 sun koma NNPP

  • Sabuwar jam'iyya mai tambarin kayan marmari na samun karuwar mambobi a jihar Jigawa, Arewa maso yammacin Najeriya
  • Jam'iyyar ta yi taron gangaminta makon da ya gabata inda ta zabi sabbin shugabanninta na tarayya
  • Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ne jagoran jam'yyar NNPP na kasa

Dutse - Jam'iyyar New Nigerian People Party (NNPP), shiyyar jihar Jigawa, ta samu sabbin mambobi 10,000 da suka gudu daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP).

Wannan mambobi sun hada da tsaffin Sanatoci, yan majalisar wakilan tarayya.

Shugaban kwamitin rikon kwaryan jam'iyyar NNPC a Jigawa, Sanata Musa Bako Aujara, ya bayyana hakan ne yayin mika ragamar mulki ga sabbin shugabannin jam'iiyyar da aka zaba, rahoton Tribune.

Yace:

"Daga cikinsu akwai tsaffin kwamishanoni, shugabannin kananan hukumomi da hadimai."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Ma'aikatan jami'a karkashin SSANU da NASU sun hargitsa jami'ar Legas

"A yau NNPP cewa zabin da yan Najeriya ke da shi, dubi ga adadin mutanen da ke shiga jam'iyyar kullum, muna kyautata zaton cewa NNPP zata mamaye Najeriya da jihohi 36 a zaben 2023."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jam'iyyar NNPP
PDP da APC sun yi babban rashi: Tsohon Sanata, tsaffin yan majalisa, mambobi 10,000 sun koma NNPP
Asali: Facebook

Jawabi a madadin masu sauya shekar, tsohon mai magana da yawun tsohon gwamna Sule Lamido, Lawan Kazaure, yace sun yi watsi da PDP ne saboda rashin alqiblarta.

Yace sun dade suna kira ga shugabannin jam'iyyar su gyara amma an yi watsi da shawararsu.

NNPP ta sayi sabbin shugabanni a Jigawa

Shugaban kwamitin rikon kwarya, Sanata Musa Bako Aujara, da yake tsokaci yayin miƙa Sakatariyar NNPP ga sabbin shugabanni, ya ce an bayyana waɗan da suka yi nasara ne ta hanyar sahihin zaɓe.

Ya yi iƙirarin cewa jam'iyyar NNPP ta kafa tsari mai kyau a jihar Jigawa, ta yanda za'a iya cewa ta shirya tsaf wajen kwace mulki daga hannun APC a babban zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Abba Gida-Gida ya sauya sheka daga PDP zuwa NNPP

Shugaban matasan jam'iyyar APC a Uk ya yi murabus, ya koma NNPP mai kayan marmari

Shugaban matasan jam'iyyar APC reshen ƙasar Burtaniya, Dakta Usman Tijjani Shehu, ya fice daga jam'iyya mai mulki, ya koma NNPP mai kayan marmari.

Ya tabbatar da murabus ɗinsa a wata wasiƙa da ya aike wa shugaban APC na gundumarsa a ƙaramar hukumar Kabo, jihar Kano kuma ya tura wa APC reshen Burtaniya kwafinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel