Karfin hali: Mace ta farko a APC ta ayyana aniyar gaje kujerar Buhari a zaben 2023

Karfin hali: Mace ta farko a APC ta ayyana aniyar gaje kujerar Buhari a zaben 2023

  • Gabannin babban zaben 2023, an samu wata mace da ta shiga tseren takarar kujerar shugaban kasa a jam'iyyar APC
  • Ibinabo Joy Dokubo, ita ce mace ta farko da ta ayyana kudirinta na son gadar Shugaba Buhari a jam'iyyar mai mulki
  • Dokubo ta sha alwashin ba bangaren ilimi, tsaro da noma fifiko idan har aka zabe ta a matsayin shugabar kasar Najeriya

Abuja - Wata yar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Ibinabo Joy Dokubo, ta ayyana aniyarta ta son tsayawa takarar kujerar shugaban kasa a 2023.

Dokubo, ita ce mace ta farko da ta shiga tseren takarar shugabancin kasar a jam’iyyar mai mulki, jaridar The Cable ta rahoto.

Karfin hali: Mace ta farko a APC ta ayyana aniyar gaje kujerar Buhari a zaben 2023
Karfin hali: Mace ta farko a APC ta ayyana aniyar gaje kujerar Buhari a zaben 2023 Hoto: The Nation
Asali: UGC

Da take jawabi a taron sanar da kudirin nata a ranar Laraba, 6 ga watan Afrilu a Abuja, Dokubo ta ce za ta kara a kan ci gaban da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kawo.

Kara karanta wannan

Sau uku Ubangiji na kirana, ya ce Atiku ne zai gaji Buhari a 2023, inji Dino Malaye

Yar takarar ta ce fannin tsaro, ilimi da noma na daga cikin bangarorin da za ta baiwa muhimmanci idan har aka zabe ta a matsayin shugabar kasar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton ya nakalto Dokunbo na cewa:

“Na tsaya a gaban wannan taro mai albarka domin ayyana kudirina na tsayawa takarar shugaban kasar Najeriya karkashin jam’iyyarmu ta All Progressive Congress (APC) mai albarka a 2023.
“Kamar yadda muke gani, tsawon shekaru bakwai da suka gabata, jam’iyyarmu mai albarka ta yi namijin kokari a dukka bangarori amma matsalar rashin tsaro da ake fama da shi a yankunan kasar musamman a arewa maso gabas da arewa ta tsakiya ya sa yan Najeriya basa ganin tarin nasarorinmu.
“Ku duba tarin ci gaba na ababen more rayuwa a bangaren hanyoyi da sashin layin dogo. A Najeriya a yau, babu wata jiha a kasar da ba ta dandani aikin gina hanya a karkashin babbar jam’iyyarmu ta APC ba.

Kara karanta wannan

Takarar shugabancin Tinubu ya samu gagarumin goyon baya daga wata kungiyar arewa

“Zan kara kan wadannan ci gaba da ake gani daga jam’iyyata ta APC. Zan tabbatar da ganin cewa an ci gaba da kula da wadannan hanyoyi da zaran an kammala su domin gudun lalacewarsu gaba daya. Hakazalika, game da hanyar layin dogo, zan tabbatar da ganin mun hada su da dukka yankunan kasar guda shida domin rage jigilar manyan motoci a hanya maimakon layin dogo.
“A matsayina na yar asalin Bakana, Kalabari, Rivers da Ijaw, zan hada yankunan ruwa zuwa cikin birni.”
'Yar takarar ta ce za ta kafa tsarin ‘saka ido na makwabta’ a matsayin wani mataki na tinkarar kalubalen tsaro da ke addabar kasar.
“Zan fahimtar da yan Najeriya cewa idan aka zabe ni, sauran matakan da nake son amfani da su don tabbatar ganin cewa an kare rayuka da dukiyoyi ba za su fadu ba a nan saboda dalilai na tsaro."
"Zan ba ilimi fifiko ta hanyar mayar da shi kyauta ga kowa da kowa ciki har da marasa galihu."

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Mai son gaje kujerar Buhari daga PDP ya hakura, ya barwa Peter Obi

2023: Muna Buƙatar Jarumai Iri Na Domin Ceto Najeriya Daga Mutuwa, In Ji Wike

A wani labarin, Nyesom Wike, gwamnan Jihar Ribas ya ce yana da iko da karfin da ake bukata a zaben shugaban kasar da zai ceto Najeriya a 2023, The Cable ta ruwaito.

Ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da jagororin jam’iyyar PDP na Jihar Gombe yayin yawon kamfen din zaben fidda gwanin jam’iyyar da ke karatowa inda ya ce Najeriya tana bukatar jajirtattu irinsa don su ceto ta daga mutuwa.

Gwamnan ya bukaci jiga-jigan jam’iyyar na jihar da su kiyaye asarar kuru’unsu wajen zaben fidda gwani ga wanda suka san ba zai iya lashe zaben kasa na 2023 ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng