Jam'iyyar APC ta gamu da cikas, Wani babban ƙusa tare da dandazon mambobi sun koma PDP
- Jam'iyyar APC mai mulki ta gamu da wani cikas a Kwara yayin da take shirin babban gangamin taro na ƙasa ranar Asabar
- Tsohon ɗan takarar gwamna kuma jigo a APC ya jagoranci dandazon masoya sun koma jam'iyyar PDP mai hamayya
- Mista Oyabambi, yace rikici ya baibaye APC a kowane mataki wanda ya hana gwamnati sauke nauyin dake kanta
Kwara - Jigon jam'iyyar APC a jahar Kwara, Otunba Adetunji Oyabambi, ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP mai hamayya tare da dandazon magoya bayansa.
Tribune Online ta rahoto cewa, Oyabambi, wanda ya nemi takarar gwamna a 2019 karkashin jam'iyyar UDP ya sanar da komawa PDP a Sakatariyar gundumar Ijagbo.
Oyabambi, wanda ya alaƙanta rashin iya shugabanci a matsayin dalilin ficewarsa daga jam'iyya mai mulki, ya caccaki gwamnatin APC da rashin jin tausayin al'umma.
A jawabinsa ya ce:
"Jam'iyyar APC tun daga matakin jiha zuwa ƙasa itace matsalar dake hana gwamnati inganta rayuwar al'umma da jagoranci na gari. Kuna ganin abin da ke faruwa a Kwara, to haka ne a sauran sassan Najeriya."
"A matakin ƙasa, APC na fama da rikici, nan a Kwara muna da ɓangarori daban-daban, kuma hakan na ɗauke hankalin gwamna, ya koma kokarin saita mambobi domin samun nasara a zaɓe na gaba."
Jam'iyyar APC ba ta da tsarin tausayin mutane
Mista Oyabambi, wanda ya samu kyakkyawar tarba daga zababbun shugabannin PDP na gunduma, ya ce APC jam'iyya ce da bata da tsayayyar manufa ga al'umma.
Ya sha alwashin cigaba da ɗumbin ayyukan alherin da ya saba na tallafawa mutanen mazaɓarsa, inda yace abun a jininsa yake, duk inda ya koma zai cigaba.
Bugu da ƙari, ya bayyana tsohon shugaban majalisar dattawa, Dakta Bukola Saraki, a matsayin mutum na gari, wanda a ko da yaushe zuciyarsa da soyayyarsa ta mutanen Kwara ce da yan Najeriya.
A wani labarin na daban kuma Shugabancin APC: Jerin Sunayen yan takarar da suka yi fatali da umarnin Buhari, suka mika Fam Hedkwata
Yayin da ranar 26 ga watan Maris da APC zaɓa don gudanar da babban taronta ke ƙara natsowa, yan takara na cigaba da cike sharudda.
Duk da wasu bayanai sun nuna shugaba Buhari ya nuna zabinsa, amma har yanzun wasu yan takara ba su hakura ba.
Asali: Legit.ng