Babu shiri, dole Shugaban PDP ya tada taro saboda za a kawo tashin hankali kan tutar 2023

Babu shiri, dole Shugaban PDP ya tada taro saboda za a kawo tashin hankali kan tutar 2023

  • Manyan jagororin jam’iyyar PDP na kasa sun yi wani zama na musamman a farkon makon nan
  • A wajen wannan taro wani Gwamna ya kawo shawarar a hana wadanda suka bi APC neman tikiti
  • Idan aka bi wannan shawara, dole PDP za tayi fatali da Atiku, Tambuwal da Saraki a zaben 2023

Abuja - Rudani ya shiga cikin babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a daren ranar Litinin, wanda hakan ya jawo Dr. Iyorchia Ayu ya dage zaman da ake yi.

Jaridar The Nation ta ce an samu sabani a jam'iyyar PDP yayin da wasu ‘yan siyasar Kudu suka nemi a hana duk wanda ya sauya-sheka tikitin yin takara.

‘Yan siyasar sun hakikance a kan cewa duk wanda ya bar jam’iyyar PDP zuwa APC a baya, bai cancanci ya zama ‘dan takarar shugaban kasa a 2023 ba.

Kara karanta wannan

Atiku ga manyan PDP: Don Allah ku kara bani dama na gwada takara a 2023 ko zan dace

Wani gwamna da ya fito daga kudancin Najeriya ne ya kawo wannan shawara da ta kawo rigima.

Za a yi waje da 'Yan Arewa daga takara

Atiku Abubakar, Bukola Saraki, Aminu Tambuwal da Rabiu Kwankwaso duk sun sauya-sheka daga PDP zuwa APC, sannan suka dawo kafin zaben 2019.

Idan aka yi amfani da wannan shawara, duk cikin wadannan ‘yan siyasa da suka fito daga Arewacin Najeriya, babu wanda PDP za ta ba tuta a 2023.

Shugabanni a PDP
Atiku, Saraki da Tambuwal Hoto: Daily Post/ www.sunnewsonline.com
Asali: UGC

An samu sabani a taron PDP

Hujjar da masu wannan ra’ayi suka rike ita ce, a dalilin sauya-shekar wadannan jiga-jigan ‘yan siyasa ne PDP ta rasa mulki, har ta zama jam’iyyar adawa.

A gefe guda akwai wadanda ba su karbi wannan magana ba, su ka nuna cewa daukar wannan shawarar ta na nufin ana bin ‘yan siyasar ne da wani kulli.

Kara karanta wannan

Rikicin APC: Kalubalen da bangaren su Shekarau za su fuskanta a siyasa kafin zaben 2023

Wata majiya ta ce akwai masu ganin tun da aka bar Atiku, Tambuwal, Saraki da Kwankwaso suka nemi tikiti a zaben da ya wuce, ba za a hana su a yau ba.

Wani babba a jam’iyyar ya maida raddi yana cewa su ne suka kafa PDP, amma yau wasu sun yi kane-kane, su na tunanin su kadai ne suka mallaki jam’iyya.

Wannan sabani ya jawo shugaban jam’iyya na kasa Dr. Iyorchia Ayu ya daga zaman. Hakan kuma ya yi sanadiyyar dakatar da zaman majalisar BOT zuwa gobe.

Su wa suka halarci taron?

Walid Jibrin; Atiku Abubakar; Sanata Ike Ekweremadu; Okwesilieze Nwodo; Bukola Saraki da Gwamnoni 10 su na cikin wadanda aka yi wannan zaman da su.

Ragowar su ne: Anyim Pius Anyim da Adolphus Wabara; Sai Ahmed Makarfi; Enyinnaya Abaribe; Abubakar Baraje; Hon. Ndudi Elumelu; da kuma Cif Bode George.

Na hana Tinubu tikiti - Atiku

Kara karanta wannan

Na kusa da Buhari ga Osinbajo da Fayemi: Tinubu ya fi karfinku a zaben 2023, ku hakura kawai

A jiya tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bada labarin yadda ya yi wa watsi da tayin da Asiwaju Bola Tinubu ya kawo masa a AC a zaben 2007.

Atiku Abubakar ya shaidawa Duniya cewaTinubu ya nemi su yi takara tare da shi a matsayin mai neman mataimakin shugaban kasa, amma sai ya dauko Ben Obi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel