Bode George: Zan tattara na koma Ghana sannan na dunga kallo daga nesa idan Tinubu ya zama shugaban kasa
- Jigon jam'iyyar PDP, Bode George, ya magantu a kan takarar da jagoran APC na kasa, Bola Tinubu, ke yi na neman kujerar shugaban kasa a zaben 2023
- Bode George ya sha alwashi tarkatawa ya bar kasar nan zuwa Ghana idan har Tinubu ya zama shugaban kasa
- Ya ce tsohon gwamnan na jihar Lagas zai daura iyalansa ne a kan manyan mukamai idan har ya cimma burinsa na zama shugaban kasa
Lagos - Jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Bode George, ya bayyana cewa zai tattara ya koma kasar Ghana idan tsohon gwamnan jihar Lagas, Bola Tinubu, ya zama shugaban kasar Najeriya a 2023, The Cable ta rahoto.
Tinubu, wanda ya kasance babban jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, ya sanar da aniyarsa ta son yin takarar shugaban kasa a babban zaben kasar mai zuwa.
Tun bayan lokacin, tsohon gwamnan na jihar Lagas da magoya bayansu sun zagaya yankuna da daman a kasar domin tattaunawa da sarakuna da masu ruwa da tsaki a harkar siyasa.
A wani taron manema labarai a Lagas a ranar Asabar, 20 ga watan Maris, George ya ce Tinubu zai tabbatar da ganin cewa ahlinsa sun dare manyan mukamai idan ya zama shugaban kasa, inda ya kara da cewar tsohon gwamnan bai cancanci hawa kujerar ba, Channels tv ta rahoto.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce:
“Ina farin ciki da cewar shugaban kasa ya sanya hannu a sabuwar dokar zabe. Idan har ya samu damar shiga Villa (Tinubu), b azan kasance a cikin kasar nan ba.
“Kuma ba wasa nake yi ba. Zan iya zuwa gana, na koma can da zama sannan na dunga kallon abubuwan da ke gudana daga nesa. Za ku ga abun da zai faru.
“Wannan dan ‘asha dadi ne a Lagas. Zai sake samar da asha dadi a wani wajen da zai kai kudadenku. Matarsa za ta zama shugabar majalisar dattawa. Dansa zai zama gwamnan Lagas. Yarsa za ta zama uwar kasuwa ta Najeriya.
“Me ya yi don tabbatar da cewar ya cancanci wani ya karrama shi a kasar nan?
“Babu wani abun san zuciya. A zahirin gaskiya, kanwata ta kira ni. Ta ce wasu mutane na rade-radin cewa ya bani kudi. Cewa Bola ya bani kudi.
“A bari ya kawo kudin. Zan fada masa ya biyo ni birnin Lagas – mutane na yunwa a nan. A nan na tashi – a birnin Lagas.”
Halin da kasa ke ciki: Ortom ya shawarci Buhari da ya yi murabus sannan ya mika mulki ga Osinbajo
A wani labarin, gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari kan jefa Najeriya a rikicin tattalin arziki da kuma gazawarsa wajen magance matsalolin tsaro a kasar.
Ortom ya yi kira ga shugaban kasar da ya yi murabus sannan ya mika mulki ga mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo.
A wata hira da Sunday Vanguard, Ortom ya kuma ce goyon bayan shugaba Buhari da ya yi don ya zama shugaban kasa a 2015 kuskure ne.
Asali: Legit.ng