Shawaran Masari ga masu rike da mukamai: Ku ajiye mukamanku kafin takara
- Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari ya bukaci masu rike da mukaman siyasa, wadanda ke da ra’ayin yin takarar mukaman gwamnati a 2023 da su yi murabus
- Masari ya umurce su da su ba dokar zabe da Buhari ya sanyawa hannu kwanan nan hadin kai
- Ya bayyana hakan ne a ranar Talata, a Katsina yayin da yake zantawa da manema labarai bayan wata ganawar sirri tare da masu rike da mukaman siyasar
Katsina - Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya bukaci masu rike da mukaman siyasa, wadanda ke da ra’ayin yin takarar mukaman gwamnati a 2023, da su bi tanade-tanaden dokar zabe.
Gwamnan ya yi kiran ne a ranar Talata, 15 ga watan Maris, a Katsina yayin da yake zantawa da manema labarai bayan wata ganawar sirri tare da masu rike da mukaman siyasar, PM News ta rahoto.
Taron ya kuma samu halartan mataimakinsa, Alhaji Mannir Yakubu, rahoton The Punch.
Ya ce:
“Na sanar da su kan wasu ci gaba a jam’iyyarmu, APC da kuma shirye-shiryenmu na zabukan karamar hukuma.
“Na bukaci wadanda ke da aniyar son yin takara a zaben 2023 da su duba dokar zabe wacce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu kwanan nan.
“Taron ya zama dole domin mu yi abun da ya dace ta hanyar mutunta dokar zaben da nufin kaucewa abin da za a iya kaucewa.
Da aka tambaye shi kan abun da yake nufi da su yi abun da ya dace, sai Masari ya ce:
"Su ba dokar zabe hadin kai.”
Sashe na 84 (12) na dokar zabe da shugaban kasa ya sanya wa hannu kwanan nan ya hana masu rike da mukaman siyasa tsayawa takara ba tare da sun yi murabus ba.
Bukola Saraki ya bayar da gagarumin shawara ga ministocin Buhari
A wani labari makamancin wannan, tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki, ya yi kirfa ga masu rike da mukamai da ke neman yin takara a zaben 2023 da su yi murabus daga mukamansu na ministoci kafin su fara neman cimma burinsu.
Saraki ya kuma soki bukatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikewa majalisar dokokin kasar inda ya nemi a gyara sashi 84 (12) na dokar zabe.
Sashin ya haramtawa masu rike da mukaman siyasa yin zabe ko kuma a zabe su a yayin tarurrukan jam’iyya.
Asali: Legit.ng