Atiku Abubakar: Yadda Tinubu ya nemi ya zama mataimakina, amma na ce ban yarda ba

Atiku Abubakar: Yadda Tinubu ya nemi ya zama mataimakina, amma na ce ban yarda ba

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce Bola Tinubu ya nemi su yi takara tare a AC
  • Alhaji Atiku Abubakar ya ce bai amince da hakan ba, sai ya dauko Ben Obi daga yankin Ibo a 2007
  • ‘Dan takarar na PDP ya kuma fadi dalilin shi na kin neman takara a lokacin Obasanjo ya na mulki

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bada labarin yadda ya yi watsi da tayin da Asiwaju Bola Tinubu ya kawo masa a zaben 2007.

Daily Trust ta ce Atiku Abubakar ya shaidawa Duniya cewa Bola Tinubu ya nemi su yi takara tare da shi a matsayin mai neman mataimakin shugaban Najeriya.

Wazirin na Adamawa bai yarda su hada tikiti da tsohon gwamnan na Legas ba. A karshe dai jam’iyyarsu ta AC ta sha kashi a hannun Ummaru ‘Yar’adua.

Kara karanta wannan

Atiku ga manyan PDP: Don Allah ku kara bani dama na gwada takara a 2023 ko zan dace

A zaben shugaban kasa na 2007, Atiku Abubakar ya zo na uku bayan jam'iyyun PDP da ANPP. Wannan ne karon farko da Atiku ya nemi shugabancin kasa.

Sharadin da Tinubu ya bada a AC

Atiku Abubakar ya dauko labarin abin da ya faru bayan ya shiga AC, ya ce Tinubu ya gindaya masa sharadin su yi takara tare, amma ya ki yarda da hakan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babban ‘dan siyasar ya ce ya zakulo Sanata Ben Obi a matsayin abokin takararsa ne saboda mutanen kudu maso gabas suna kukan ba a tafiya tare da su.

Atiku Abubakar da Tinubu
Atiku Abubakar da Bola Tinubu Hoto: www.thisdaylive.com
Asali: UGC

“Wasu daga cikin mutanen kudu maso gabas su na kukan ba a damawa da su. A lokacin da na shiga jam’iyyar AC da abokina Tinubu ya kafa, ya bani sharuda.
“Daga cikin sharudan samun tikiti shi ne in tsaida shi a matsayin ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa. Sai na ce a’a, ba zan ba ka takara ba, na dauki Ben Obi.”

Kara karanta wannan

Rikicin APC: Kalubalen da bangaren su Shekarau za su fuskanta a siyasa kafin zaben 2023

Takara da Obasanjo

Da yake yi wa ‘yan BOT-PDP jawabi, Guardian ta ce Atiku ya ce jam'iyyarsu ta na bin tsarin karba-karba, don haka ne ya ki yarda ya yi takara da Obasanjo a 2003.

“Da yawanku ku na cikin gwamnatinmu a lokacin da duka gwamnonin PDP suka same ni a zaben 2003, suka fada mani cewa in yi takara, sai na ce masu a’a.”
“Mun yarda cewa mulki zai zauna a yankin kudu maso yamma, saboda me zan yi takara?”

- Atiku Abubakar

Batun takarar Osinbajo

A farkon makon nan rade-radi suka fara zagaye gari maganar takarar mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo a zaben da za ayi a 2023, ta na kara karfi.

A jiya Mai taimakawa mataimakin shugaban na Najeriya wajen hulda da jama’a da watsa labarai, Laolu Akande ya ce wadannan rahotannin ba gaskiya ba ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel