Atiku ga manyan PDP: Don Allah ku kara bani dama na gwada takara a 2023 ko zan dace

Atiku ga manyan PDP: Don Allah ku kara bani dama na gwada takara a 2023 ko zan dace

  • Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya ayyana kudirinsa na yin takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023
  • Atiku ya roki shugabannin jam'iyyar PDP da su sake bashi dama domin ya daga tutar jam'iyyar a zabe mai zuwa
  • Ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 15 ga watan Maris, yayin wata ganawa da shugabannin APC a Abuja

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya sanar da kwamitin amintattu na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) aniyarsa na son tsayawa takarar shugaban kasa a babban zaben 2023.

Ya bayyana kudirin nasa ne a ranar Talata, 15 ga watan Maris, yayin wata ganawa da shugabannin APC a Abuja, Channels tv ta rawaito.

Atiku wanda ya kasance dan takarar babbar jam’iyyar adawar a zaben 2019, ya roki a sake bashi dama domin ya wakilci PDP a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

2023: Jerin mutane 5 da suka bayyana aniyarsu ta yin takarar gujerar gwamnan Kaduna zuwa yanzu

Atiku ga manyan PDP: Don Allah ku kara bani dama na gwada takara a 2023 ko zan dace
Atiku ga manyan PDP: Don Allah ku kara bani dama na gwada takara a 2023 ko zan dace Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Ya yi alkawarin gina kyakkyawar alaka a fadin yankunan kasar idan har aka bashi tikitin takarar jam’iyyar yayin da yan Najeriya za su jefa zabe a shekara mai zuwa.

Ya fadama taron shugabannin PDP a taron cewa:

“Dan Allah ku hada hannu da ni wajen gina gadaje a fadin kasar nan domin kowani yanki na kasar nan ya ji ana damawa da shi.
“Shugabanni, dattawa, hazikan mutanen wannan jam’iyya tamu mai albarka, ina kira gareku da ku yi hakuri dan Allah ku sake bani dama domin ci gaba da duk wasu manufofin jam’iyyarmu domin mu tabbatar da dimokuradiyya, hadin kai, da ci gaban kasarmu.”

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi godiya ga shugabannin PDP da suka amsa gayyatarsa na halartan taron.

A karshen taron, ya je shafinsa na soshiyal midiya inda ya wallafa hotunan ganawar tasu.

Kara karanta wannan

Saura kwanaki 11 a shirya zaben shugabanni, kan jam’iyyar APC ya kara tarwatsewa

Diyar jagoran APC na Kasa Bola Tinubu ta yi tsokaci kan takarar mahaifinta a zaben 2023

A wani labarin, Folashade Tinubu-Ojo, ɗiyar tsohon gwamnan jihar Legas Bola Tinubu, ta bayyana cewa mahaifinata na da ƙosasshiyar lafiyar da zai jagoranci Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ɗiyar Tinubu ta yi wannan furucin ne yayin da mutane ke nuna damuwarsu kan lafiyar mahaifin nata.

Tun a watan Janairu, Mahaifinta ya bayyana wa manema labaran gidan gwamnati cewa ya sanar da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, kudirin gaje kujerarsa a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng