Ricikin PDP: Gwamnan Edo ya caccaki Wike kan kalamansa, yace PDP ba ta mutum ɗaya bace
- Gwamnan Edo, Godwin Obaseki, ya ɗau zafi game da kalaman wuce gona da iri da gwamna Wike na Ribas ya yi a kan siyasar Edo
- Obaseki ya yi kira ga uwar jam'iyyar PDP ta ƙasa ta umarci Wike ya shiga taitayinsa ko kuma ya koya masa darasi
- A cewarsa, Wike na da damar yin amfani da duk abin da ya mallaka wajen cimma kudirinsa amma ba ta hanyar barazana ba
Edo - Rikici tsakanin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, da takwaransa na jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ƙara tsakananta yayin da suka fara musayar yawu.
The Nation ta rahoto cewa Obaseki ya maida martani kan kalaman da gwamnan Ribas ya yi akansa da kuma mataimakinsa, Philip Shaibu, inda ya ce jam'iyyar PDP ba ta Wike ba ce shi kaɗai.
Gwamnan jihar Edo ya bayyana cewa ba zai lamurci tsangwama da wuce gona da iri a siyasa ba, ya kuma gargaɗi Gwamna Wike da ya shiga taitayinsa domin ya iya gyara wa shugabanni zama.
Obaseki ya kuma jaddada masa cewa jiharsa ta Edo ta fi karfin ya mallake ta da wata barazanar da ya saba yi wa mutane.
Haka nan a bayanan sa, gwamna Edo ya kuma zargi Wike da rashin ganin girman kowa da kuma ƙoƙarin tarwatsa jam'iyya, inda ya roki shugabannin PDP su gaggauta dakatar da shi.
Da yake kare mataimakinsa bisa kalaman da ya yi game da jam'iyyar PDP a Edo, Obaseki ya ce kamata ya yi Wike ya yi koyi da yadda shugaban PDP na ƙasa, Dakta Iyorcha Ayu, ya ɗauki maganar Mista Shaibu.
A kalaman mista Shaibu da suka jawo wannan cece-kuce, yace,, "Jagorori, shugabanni da mbobin jam'iyya waɗan da suka sauya sheƙa tare da shi daga APC, ba'a karɓe su hannu biyu ba a PDP."
Gwamnan ya nuna tsantsar mamakinsa kan ko meyasa a ko da yaushe Wike ba shi da aikin yi sai yi wa jam'iyya da shugabanni barazana.
Kana da damar yin takara - Obaseki
A cewarsa ba bu mai ja da kudirin Wike na neman takarar shugaban ƙasa a 2023, amma ba ta irin wannan halin ya dace ya biyo ba.
The Cable ta rahoto Gwamna Obaseki ya ce:
"Wike na da damar amfani da duk abin da yake da shi wajen cika burinsa, ba zai yuwu ya yi yunkurin yiwa wasu barazana da tilasta musu bin abinda yake so ba. Edo ta fi karfin haka."
A wani labarin kuma Ɗan takarar shugaban ƙasa kuma jagoran APC na ƙasa, Bola Tinubu, ya ce wajibi APC ta fita tsara a cikin sauran jam'iyyu
Jagoran APC na ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce ya zama wajibi APC ta fita tsara wajen tafiyar da harkokinta na cikin gida.
Ɗan takarar shugaban ƙasan ya yaba wa Buhari kan nuna yaƙininsa a APC da kuma kokarin kare ta daga tarwatsewa.
Asali: Legit.ng