APC ce zabin yan Najeriya kuma zamu lallasa jam'iyyu a zaben 2023, Gwamna El-Rufa'i

APC ce zabin yan Najeriya kuma zamu lallasa jam'iyyu a zaben 2023, Gwamna El-Rufa'i

  • Gwamnan Kaduna ya yi ikirarin cewa har yanzun yan Najeriya ba su da zaɓin da ya zarce jam'iyyar APC, kuma zata ci zabe a 2023
  • Malam Nasiru El-Rufa'i ya ce duk da mutane sun tsammaci abin da ya fi haka, amma idan aka kwatanta ba kamar APC
  • Ya ce ba ya sha'awar neman wata kujerar siyasa a shekarar 2023, bayan kammala mulkin Kaduna yana son hutu

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, ya ce har yanzun jam'iyyar APC ce zabin yan Najeriya nagari yayin da zaɓen 2023 ke kara matsowa.

Gwamnan ya yi ikirarin cewa jam'iyyarsa ta All Progressive Congress ce zata samu nasara a zaben shugaban kasa dake tafe.

El-Rufa'i ya yi wannan furucin ne ranar Laraba, yayin zanta wa da kafar watsa labarai ta Channels tv, ya kuma bugi ƙirjin cewa sauran jam'iyyu ba zasu iya kamo inuwar APC ba.

Kara karanta wannan

El-Rufai: Idan Buhari Ya Matsa, Zan Yi Takarar Shugaban Ƙasa a 2023 Amma Ba Don Ina So Ba

Gwamnan Kaduna, Malam El-Rufa'i
APC ce zabin yan Najeriya kuma zamu lallasa jam'iyyu a zaben 2023, Gwamna El-Rufa'i Hoto: Nasiru El-Rufai/Facebook
Asali: Facebook

A kalamansa, gwamnan ya ce:

"Ina tunanin yan Najeriya sun yi tsammanin abun da ya fi wanda muka yi, duk da haka idan suka yi nazari a tsanake su sanya sikeli da sauran jam'iyyu, mu ne dai zabin su nagari."

APC zata sake lashe zaben shugaban kasa - Elrufa'i

Tsohon ministan babban birnin tarayya Abuja ya ƙara da cewa ya na da kwarin guiwar jam'iyyarsa zata sake lashe manyan zaɓuka a 2023.

"Ina da yaƙinin a 2023, jam'iyyar APC zata lashe zaben shugaban ƙasa da kuma mafi yawancin zaɓen gwamnoni a jihohin Najeriya."

Ba na sha'awar neman wani muƙami a 2023 - Malam Nasiru

Gwamnan ya bayyana cewa ba ya sha'awar neman wata kujerar siyasa a 2023, a cewarsa bayan kammala mulkin Kaduna yana son hutu.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya bada umurnin cire Buni, ya so ya ha'ince mu: El-Rufai

"Na faɗa na sake faɗa cewa ba zan nemi takara ba, ba na sha'awar kowace siyasa. Idan Rotimi Amaechi na sha'awar neman wata kujera ya na da damar yin haka. Amma ni ba zan nemi komai ba."

A wani labarin na daban kuma Wani mutumin Kano ya fara tattaki daga Abuja zuwa Legas don goyon bayan Tinubu ya gaji Buhari a 2023

Wani mutumi ɗan asalin jihar Kano ya kuduri aniyar yin tattaki tun daga Abuja zuwa Legas domin nuna wa Tinubu ana tare.

Hussein Lawan ya ce zai yi wannan sadaukarwa ne a madadin matasa ya roki Tinubu ya fito takara don tallafawa matasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262