2023: Wani Farfesan Najeriya Ya Yunƙuro, Zai Nemi Kujerar Buhari a Ƙarkshin Jam'iyyar APC
- Godspower Ekuobase, Farfesa a Jami'ar Benin ya ayyana niyarsa na shiga takarar shugabancin kasar Najeriya a karkashin jam'iyyar APC a 2023
- Farfesa Ekuobase ya bayyana hakan ne a garin Benin yayin wani taron manema labarai inda ya gargadi mutane su dena zaben wadanda kudi kawai suka iya bada wa amma babu aiki
- Ya ce idan an zabe shi zai mayar da hankali a kan noma, tsaro, samar da ayyukan yi, ilimi, lafiya, fasaha da wasu abubuwan na inganta kasa
Benin - Wani Farfesa a Jami'ar Benin, Godspower Ekuobase, ya shiga jerin masu neman takarar shugabancin kasa a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Daily Trust ta rahoto.
Farfesan ya gargadi yan Najeriya su guji karbar kudi daga hannun yan takara wadanda ba su da wani abin alheri da za su yi wa yan kasar sai dai su siya kuri'a daga bisani su wawushe kudin kasa.
Shehu Sani: Duk mai sha'awar shiga yakin Ukraine kuma bai da $1k na biza, ya zo Arewa ya nuna kwarewarsa a yaki
A rika zaben wadanda suka iya aiki ba masu rabon kudi kawai ba, Ekuobase
Da ya ke magana da manema labarai a Benin, Jihar Edo, ya koka kan yadda yan Najeriya suke mayar da hankali kan yan siyasa masu kudi amma babu aikin da za su tsinana.
Farfesan ya ce lokaci ya yi da ya dace a bawa wadanda suka san makamashin aiki damar su jagoranci kasar.
Ya ce:
"Najeriya ba ta sayarwa bane; ba mutanen da ke da kudi muke so ba, masu kwakwalwa da kaunar kasa muke so. Idan kace kana neman mutum mai kudi, zai so ya mayar da kudinsa. Ba sayar da Najeriya za mu yi."
Rashin shugabanci nagari ya mayar da Najeriya baya, In ji Ekuobase
Ya ce kasar ta tsinci kanta a inda ta ke ne saboda irin shugabannin da ake zaba wadanda kudi kawai suke da shi a maimakon masu ilimi, rahoton Daily Trust.
Ekuobase ya ce Najeriya ta zama koma baya ne saboda irin shugabanni marasa kwarewa da suka jagorance ta.
Ya ce idan an zabe shi zai mayar da hankali a kan noma, tsaro, samar da ayyukan yi, ilimi, lafiya, fasaha da wasu abubuwan don ganin Najeriya ta bunkaa ta zama kasa mai sarrafa abubuwa ba saya kadai ba.
2023: Za mu bi didigin inda ƴan takara suke samo kuɗi, za mu sa ido kan asusun bankin ƴan siyasa, INEC
A wani rahoton kun ji cewa Hukumar zabe mai zaman kanta na Najeriya, INEC, ta aika da muhimmin sako ga yan siyasa da jam'iyyun siyasa gabanin babban zaben shekarar 2023.
Hukumar ta sha alwashin cewa za ta saka idanu a kan 'yan siyasa da jam'iyyun siyasa domin gano inda suke samo kudade domin yakin neman zabe, Vanguard ta ruwaito.
Shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya bayyana hakan yayin wani taro da hukumar zaben ta shirya a Abuja, ranar Juma'a 21 ga watan Janairu, kuma ya ce hukumar za ta saka ido kan yadda aka hada-hadar kudade ranar zabe don dakile siyan kuri'u, Daily Trust ta ruwaito.
Saurari karin bayani ...
Asali: Legit.ng