Tsohon Shugaban Banki, Hayatu-Deen, Ya Shiga Jerin Masu Neman Gadon Kujerar Buhari
- Tsohon mamallaki kuma manajan darekta na Bankin FSB, Alhaji Mohammed Hayatu-Deen, ya bayyana ra’ayin sa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 karkashin jam’iyyar PDP
- Ya tara dubbannin magoya bayansa da ke Legas inda ya bayyana kudirin sa na takarar don bunkasa kasa da kuma samar da mafita ga matsalolin da Najeriya take fuskanta
- Kamar yadda Hayatu-Deen ya shaida, kasar nan tana bukatar shugaba na kwarai wanda ya goge ya kuma ratsa wurare daban-daban ta yadda zai sanya gogewarsa a shugabancinsa
Legas - Tsohon mamallaki kuma manajan darekta na FSB international Bank, Alhaji Mohammed Hayatu-Deen, ya bayyana kudirin sa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 karkashin inuwar jam’iyyar PDP.
Ya sanar da burin sa na tsayawa takara a Legas yayin da yake yi wa dubbannin masu mara masa baya jawabi a Legas, Daily Trust ta ruwaito.
A cewarsa, zai tsaya takara tare da sauran ‘yan takarar jam’iyyar PDP wadanda yanzu haka suka bayyana kudirin su.
Yana burin ganin ya kawo ci gaba ga Najeriya
Daily Trust ta rahoto yadda ya ce yana sha’awar tsayawa takarar ne don ganin ya kawo gyara ga kasar nan ta hanyar kirkira da samar da ci gaba ga mutanen Najeriya don kasar ta bunkasa.
Hayatu-Deen, wanda masani ne a harkar tattali ya ce kasar nan tana bukatar shugaba na daban wanda yake da hazaka, salo, dabaru da jajircewa wanda zai kawo bunkasa ga tattalin arzikin kasa.
Yayin jawabi ga mutane, ya ce yana da kudirin kawo karshen yunwa, talauci, cutuka da kuma rashin tsaro wanda yace su ne manyan matsalolin Najeriya.
Kamar yadda ya shaida:
“Na yarda da cewa ni ne mutumin da zai yi salon shugabanci na daban cike da gaskiya, jajircewa da kuma gogewa.
“Kasar nan tana fuskantar kalubale iri-iri. Sakamakon mu’amalar da nayi da mutane mabambanta, yawon da nayi a kasashen da ke nahiyar Afirka da duniya, ina da gogewar da zan kawo mafita ga mutanen Najeriya.”
Zai hada kai da kasashen waje wurin bunkasa Najeriya
Ya ci gaba da cewa:
“Mun fi ko wanne yanki hazaka da dagewa idan a harkar sana’a ne. Idan Najeriya ta samu dama, za ta bunkasa matuka. Ina so in ba ‘yan Najeriya damar bayyanar da baiwar da Ubangiji ya ba su ta hanyar kafa kamfanoni, nuna jajircewa da kuma nuna bajimtar su a fannin kirkira.”
Yayin tattaunawa akan matsalar tsaro, ya ce gwamnatin sa za ta kawo mafita mai yawa dangane da rashin tsaron da ya addabi kasa.
Kasancewar sa masani a fannin tattali, ya ce zai hada kai da kasashen ketare da ‘yan kasuwa don su sanya hannu Najeriya ta samu ci gaba mara misaltuwa.
2023: Ƙungiyar musulmai ta buƙaci Gwamna Ugwuanyi ya fito ya nemi kujerar Buhari
A wani rahoton, kungiyar hadin kan al’ummar musulmi, UMUL ta bukaci dan kabilar Ibo ya tsaya takarar shugaban kasa idan 2023 ta zo, The Sun ta ruwaito.
Kungiyar ta musulmai ta ce lokaci ya yi da cikin yankuna biyar da ke kasar nan, ko wanne yanki zai samu adalci da daidaito da juna, hakan yasa take goyon bayan Igbo ya amshi mulkin Najeriya.
Kamar yadda kungiyar ta shaida, dama akwai manyan yaruka uku a Najeriya, Hausa, Yoruba da Ibo, don haka in har ana son adalci, ya kamata a ba Ibo damar mulkar kasa don kwantar da tarzomar da ke tasowa.
Asali: Legit.ng