2023: Masu neman takara 33 ke zawarcin tikitin gwamna na APC a wata jihar arewa
- Gabannin babban zaben 2023, masu neman takara 33 sun nuna ra'ayinsu na son mallakar tikitin gwamna karkashin APC
- Shugaban jam'iyyar a Benue, Austin Agada, ya ce akwai karin mutane da za su nuna ra'ayinsu kan kujerar a kwanaki masu zuwa
- Ya kuma ce tuni sabbin shugabannin da aka rantsar suka kama aiki don ganin sun kwace kujerar gwamnan jihar a 2023
Benue - Akalla masu neman takara 33 ne suka nuna ra’ayinsu na son mallakar tikitin gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Benue.
Shugaban APC a jihar, Kwamrad Austin Agada, ya bayyana a Makurdi a ranar Laraba, 23 ga watan Fabrairu, cewa karin masu neman takara za su ayyana aniyarsu a kwanaki masu zuwa, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Agada ya ce:
“A yanzu muna da mutane 33 da suka nuna ra’ayinsu a kan tikitin gwamna karkashin inuwar APC. Akwai karin mutanen da za su nema a nan gaba.”
Agada ya kuma bayyana cewa za a ba dukkanin masu neman takarar filin fafatawa domin su gwada sa’arsu da shahararsu a cikin mutane.
Shugaban jam’iyyar ya kara da cewar sabbin shugabanni da aka rantsar sun dade da fara aiki ba ji ba gani domin ganin APC ta dare kujerar gwamna a babban zaben 2023.
Kwamishinan gwamnan APC ya fice daga jam'iyya, ya koma PDP
A wani labarin, kwamishinan harkokin waje na jihar Imo da ya sauka, Fabian Ihekweme, ya fice daga jam'iyyar APC ya koma PDP mai hamayya.
Vanguard ta rahoto cewa an gudanar da bikin sauya shekan a filin Nwankwo, Owerri babban birnin jihar, ranar Laraba 23 ga watan Fabrairu 2022.
Shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu, shi ne ya jagoranci jiga-jigan PDP na ƙasa zuwa taron tarban masu sauya shekan, wanda PDP ta shirya a Owerri.
Asali: Legit.ng