Bikin sauya sheka: Tsohon mataimakin kakakin majalisa, hadimin ministar Buhari sun bar APC zuwa PDP
- Jam’iyyar APC ta rasa wasu manyan jiga-jiganta a jihar Kwara inda suka koma PDP
- Daga cikin jiga-jigan jam’iyyar mai mulki da suka fice harda tsohon mataimakin kakakin majalisar Kwara, Abubakar Shuka Baba da hadimin ministar Buhari, Aliyu Ibrahim Wure
- Shuka Baba ya ce sun koma jam’iyyar adawa ne bayan APC ta ki mika tikitinta na takarar gwamna a zaben 2023 ga yankin Kwara ta Arewa
Kwara - Gabannin zaben 2023, tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kwara, Rt. Hon. Abubakar Shuka Baba, da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar APC a karamar hukumar Kaima ta jihar sun sauya sheka zuwa PDP.
Hadimin karamar ministar sufuri, Sanata Gbemisola Saraki, Alhaji Aliyu Ibrahim Wure, shima ya fice daga jam'iyyar mai mulki, rahoton Thisday.
Saran shugabannin APC da suka sauya sheka sun hada da tsohon shugaban karamar hukuma, Alhaji Haliru Madugu; tsohon mataimakin shugaban karamar hukuma, Alhaji Usman Yusuf, da Alhaji Dantalo Yaro.
Har ila yau, mambobin jam’iyyar APC a gudunmar Womi/Ayaki a karamar hukumar Moro da ke jihar sun koma babbar jam’iyyar adawar kasar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An tattaro cewa sauya shekar jiga-jigan na APC zuwa PDP baya rasa nasaba da mika tikitin takarar da jam’iyyar adawar ta yi zuwa yankin kwara ta arewa.
Kafin sauya shekarsu, shugaban jam’iyyar a jihar kuma tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da wasu shugabannin jam’iyyar sun ta janyo mutane a kokarinsu na kwace mulki daga APC a babban zaben jihar mai zuwa.
Dalilin da yasa muka koma PDP - Shuka Baba
Da yake magana a wani taron maraba zuwa da aka shirya masu a Kaima, Shuka Baba, ya bayyana cewa sun yanke shawarar barin APC zuwa PDP ne domin yin aiki tare da sauran mambobin jam’iyyar adawar bayan ta mika tikitinta na gwamna zuwa Kwara ta Arewa.
Ya ce za su tattaro mutanen yankin domin lashe zaben, domin a cewarsa an hana mutanen yankin shugabantar jihar a shekarun da suka gabata.
Baba ya ce:
“Mun yanke shawarar cewa duk jam’iyyar siyasar da ta mika tikitin gwamnanta zuwa yankin za mu koma cikinta, kuma shine abun da muke yi a Kaima a yau.”
Don haka, ya ce zai hada hannu da shugabannin PDP domin kwace mulki daga APC a zaben jihar mai zuwa.
Thisday ta kuma rahoto cewa da yake tarbar masu sauya shekar a madadin shugaban jam'iyyar PDP na jiha, Rt. Hon. Babatunde Mohammed, da ‘yan takarar gwamna hudu na jam’iyyar PDP daga mazabar Kwara ta Arewa, sun ce su kalli dawowar su PDP tamkar komawa gida ne.
Gaba ta kai ni: Bayan barın PDP zuwa APC, Sanata ya tashi da babban matsayi a majalisar dattawa
A wani labari na daban, mun ji cewa Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya nada tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Emmanuel Bwacha, a matsayin shugaban kwamitin sayan kayayyaki na majalisar dattawa.
An sanar da nadin Bwacha ne a zauren majalisar a yau Laraba, 9 ga watan Fabrairu, jaridar Vanguard ta rahoto.
A makon da ya gabata ne, dan majalisar ya sauya sheka daga babbar jam’iyyar adawa ta People’s Democratic Party (PDP) zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Asali: Legit.ng