Ganduje ga 'yan tsagin Shekaru: Kawai ku amince kun sha kaye, ku zo mu hada kai
- Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya magantu bayan cin nasara a kotu kan batun shugabancin APC a Kano
- Gwamnan ya yi kira ga magoya bayan Shekarau da su amince sun sha kaye, kuma su zo su hade dashi
- Ya bayyana cewa, hade kai da juna tsakaninsu ne zai iya kawo wa jihar ci gaba ta fuskoki da yawa na siyasa
Jihar Kano - Rahoton jaridar Daily Trust ya ce, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano ya yi kira ga tsagin APC na jihar karkashin Sanata Ibrahim Shekarau da su amince da shan kaye, su hada kai da gwamnatinsa domin ciyar da Kano gaba.
Ganduje ya yi wannan kiran ne a jiya Lahadi a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin jam’iyyar na mazabu 484 da ke jihar a dakin taro na Coronation da ke gidan gwamnati.
Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja, a ranar Alhamis ta yi watsi da hukuncin karamar kotun da ta bai wa tsagin Shekarau nasara tare da ayyana tsagin Gwamna Umar Ganduje a matsayin sahihin tsagi.
Sai dai, da sauran rina a kaba, domin kungiyar G-7 ta tsagin Shekarau ta sanar da yanke daukaka kara zuwa kotun koli.
Ganduje ya ce bangarensa da na Shekarau iyayensu daya ne, inda ya bayyana cewa idan aka hada kai za su iya ciyar da jihar da jam’iyyar gaba.
Gwamnan ya ce:
“Kano ce ta fi kowace jiha farin jini a fagen zabe, ita ce cibiyar kowane dan takara kuma kowa yana zuba mata ido. Shi ya sa muke fuskantar kalubale lokaci zuwa lokaci. Amma a wannan karon, kotun ta gama da komai.
“Ina kira ga ’yan uwanmu, abokan aikinmu, da G-7 da su dawo mu gina jam’iyyarmu tare. Kofofinmu a bude suke ga duk wanda ke son shiga jam’iyyar daga ko’ina domin a shirye muke mu tabbatar da samun nasara a kowane mataki na zabe mai zuwa.”
Gwamna Ganduje ya ce duk da irin gwagwarmayar da ake yi na ganin jam’iyyar ta samu nasara, gwamnatinsa ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen gudanar da ayyukan alheri da take yi wa jihar, yana mai tabbatar da cewa ya himmatu wajen kara kaimi musamman a yankunan karkara.
Shugaban APC na Kano ya magantu
Tun da farko shugaban jam’iyyar APC a jihar Kano Alhaji Abdullahi Abbas, ya godewa shugabannin jam’iyyar daga matakin jiha zuwa shiyya bisa goyon bayan da suke ba shi.
Ya kuma yi alkawarin hada kai da duk wasu shugabannin jam’iyyar domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da yin kira ga ‘yan jam’iyyar da su hade domin ciyar da jam’iyyar da jihar Kano gaba.
Kisan Hausawa dillalan shanu a Kudu: Kungiyoyin Arewa sun fusata, sun tura gargadi ga gwamnatin Abia
Jaridar Nigerian Tribune ta rahoto kalaman shugaban na APC, inda yake cewa:
“Abin da ke faruwa a tsakaninmu da tsagin Shekarau ba komai ba ne illa rikicin cikin gida na jam'iyya kamar yadda aka saba da kuma sanannen abu a tsarin dimokuradiyya.
"Ina ganin zamanin amfani da kalamai na batanci ya kare, don haka ya kamata mu hada kai mu gina abin a zo a gani wanda zai jure jarabawar zamani."
Jagororin Kwankwasiyya sun juyawa Kwankwaso baya, ana kishin-kishin za su tsallaka APC
A wani labarin, tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Mu’az Magaji wanda aka fi sani da ‘Dansarauniya, ya kyankyasa samun wasu sababbin shiga cikin APC.
Injiniya Mu’az Magaji ya fito shafinsa na Facebook a ranar Juma’ar da ta wuce ya na cewa wasu jagororin bangaren Kwankwasiyya, su na shirin shigowa jam’iyyar APC.
Magaji ya ce tsaginsu na G7 zai kara yawa a yayin da suke sauraron shigowar wasu manyan ‘yan adawa. 'Yan G7 su na karkashin jagorancin Malam Ibrahim Shekarau.
Kaduna: Kotun Shari'a Ta Tura Kishiyoyi 2 Zuwa Gidan Yari Saboda Faɗa Kan Mijinsu, Mijin Ya Ce Akwai Yiwuwar Ya Sake Su Duka
Daga cikin wadanda za su tsallako zuwa bangaren G7 a cewar tsohon kwamishinan akwai Dr. Yunusa Dangwani, Aliyu Madakin Gini, da kuma Dr. Yusuf Danbatta.
Asali: Legit.ng