Abin Da Yasa APC Ta Sha Kaye a Zaɓen Ƙananan Hukumomin Abuja, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa, Dauda

Abin Da Yasa APC Ta Sha Kaye a Zaɓen Ƙananan Hukumomin Abuja, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa, Dauda

  • Dr Ibrahim Bello Dauda, Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar APC a 2023, ya nuna rashin jin dadinsa kan kayen da APC ta sha a zaben kanana hukumomi na Abuja
  • Bello Dauda ya ce rashin hadin kai tsakanin 'ya'yan jam'iyyar na APC ne ya janyo musu shan kayen ya kuma ce ya kamata sauran yan jam'iyyar su dauki darasi gabanin babban zaben 2023
  • Dan takarar shugaban kasar ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari da hukumar INEC bisa gudanar da zabe na adalci

Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar APC a 2023, Dr Ibrahim Bello Dauda, ya koka kan rashin kwazon da APC ta yi a zaben kananan hukumomi da aka yi a Abuja a ranar Asabar ya bukaci jam'iyyar ta koyi darasi gabanin babban zaben 2023.

Kara karanta wannan

Matasa Sun Yi Wa Ministar Buhari Ihun ‘Ba Ma So’ a Birnin Tarayya Abuja

Dauda, wanda ya ce yan jam'iyyar ba su hada kansu ba yayin zaben na Abuja, amma, ya jinjinawa Shugaba Muhammadu Buhari da hukumar INEC saboda adalci da zabe cikin lumana a Abujan, rahoton Vanguard.

Abin da yasa APC ta sha kaye a zaben kananan hukumomi na Abuja, Dan takarar shugaban kasa, Dauda
Dan takarar shugaban kasa, Dauda: Abin da yasa APC ta sha kaye a zaben kananan hukumomi na Abuja. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Sai dai Dauda ya yi korafi kan rashin fitowa zabe da mutane ba su yi ba.

Ya kuma taya wadanda suka yi murna a zaben nasara, yana mai cewa su dauki nasararsu a matsayin kira domin yi wa al'umma hidima a mazabunsu.

Sakamakon zaben na Abuja

Babban jam'iyyar hamayya ta PDP ce ta fi nasara inda ta lashe zaben ciyamomin kananan hukumomi uku cikin shida sannan ta lashe kujerun kansila 44. APC a lashe zaben ciyamomi uku da kujerun kansila 18.

A sanarwar da direktan watsa labaransa na yakin neman zaben mai suna El Dabi 2023, Dauda ya ce sakamakon ya nuna cewa INEC da Buhari sun mayar da hankali don ganin an yi tsaftaccen zabe.

Kara karanta wannan

Ku mika wuya tun kafin mu iso maɓoyarku, Sabon Kwamishina ya aike da sako ga yan bindiga

A cewar dan kasuwar mai shekara 49, Shugaban kasar ya nuna kamun kai ta yadda bai yi katsalandan a zaben ba ya bari yan Najeriya suka zabi abin da suke so, rahoton Vanguard.

Dauda ya ce:

"Ganin cewa jam'iyyar shugaban kasa ba ta lashe dukkanin kujerun zaben Abuja ba alama ce da ke nuna demokradiyyar mu na kan tsari mai kyau."

Yan Najeriya za su iya barci da idonsu biyu, tunda sun san cewa kamar zaben Edo, shugaban kasa ba zai yi katsalandan a zaben ba. Shugaban kasar da INEC suna barin a yi adalci a bawa mutane wanda suka zaba.

Kazalika, Dauda ya ce 'yan APC ya kamata su koyi darasi su hada kansu su tunkari zaben a matsayinsu na tsintsinya madaurinki daya.

"Idan za a fadi gaskiya, APC ba ta yi kokari ba a zaben ranar Asabar, " a cewarsa.
"Hakan na nufin ya zama dole mu hada kan mu wuri guda, APC a kananan hukumomin ba su hada kansu ba. Wannan kuma darasi ne ga sauran jam'iyyar a zaben da ke gaba."

Kara karanta wannan

Shugaban kasa yana tsaka-mai-wuya ana saura kwana 8 zaben shugabannin APC

Dauda ya kuma koka kan karancin mutane da suka fito zaben.

2023: Magoya bayan Atiku sun buƙaci ya haƙura da takara, ya goyi bayan ɗan takara daga kudu

A wani labarin, Gamayyar kungiyoyin masu goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar sun shawarci Turakin na Adamawa ya hakura da yin takarar shugaban kasa a 2023 amma ya goyi bayan dan takara daga kudu maso gabashin kasar.

Kungiyoyin sun hada da Middle Belt Network for Atiku, North For North Support Group for Atiku, Turaki Arewa Vanguard for Atiku da South-West Development Frontiers, The Cable ta ruwaito.

Atiku bai riga ya bayyana cewa zai fito takarar shugaban kasar ba a hukumance amma ana hasashen yana shirin sake neman kujerar shugaban kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164