Matasa Sun Yi Wa Ministar Buhari Ihun ‘Ba Ma So’ a Birnin Tarayya Abuja

Matasa Sun Yi Wa Ministar Buhari Ihun ‘Ba Ma So’ a Birnin Tarayya Abuja

  • Matasa sun yi karamar ministan babban birnin tarayya Abuja, Hajiya Ramatu Tijjani Aliyu, ihun ba ma so a yayin bikin mika satifiket ga zababun ciyamomi
  • Hakan ya faru ne a lokocin da ministan ke jawabi ta kuma shawarci INEC ta gano sabuwar hanyar da mutane za su iya kada kuri'a idan na'uarar zamani ta BVAS ta samu matsala
  • Hakan ne ya sa matasan suka rika ihun 'karya ne ba ma so' duk da kokarin da ministan ta yi na yin karin bayani har dai dole ta ajiye abin magana ta koma ta zauna kafin daga bisani ta tafi

Abuja - An yi wa karamar ministan babban birnin tarayya Abuja, FCT, Hajiya Ramatu Tijjani Aliyu, a yayin da ta ke mika satifiket ga zababbun shugabannin kananan hukumomi a Abuja.

Kara karanta wannan

Ku mika wuya tun kafin mu iso maɓoyarku, Sabon Kwamishina ya aike da sako ga yan bindiga

Kwamishinan zabe a babban birnin tarayyar, Alhaji Yahaya Bello, ya mika takardun shaidan lashe zabe ga zababbun shugabannin a taron da manyan yan siyasa suka halarta, rahoton Daily Trust.

Matasa Sun Yi Wa Ministar Buhari Ihun ‘Ba Ma So’ a Birnin Tarayya Abuja
An Yi Wa Ministar Buhari Ihun ‘Ba Ma So’ a Birnin Tarayya Abuja. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abin da yasa aka yi wa ministan ihu a wurin taron

Wasu magoya bayan jam'iyya sun datse jawabin Tijjani a lokacin da ta shawarci Hukumar INEC ta gano hanyar da mutane za su yi zabe da takarda idan na'urar lantarki na zabe ta samu matsala.

An samu wuraren da aka yi korafi kan na'urar BVAS ta INEC a zaben na kananan hukumomi a Abuja.

Magoya bayan sun rika ihu suna cewa 'Karya ne ba ma so'.

Ministan ta yi kokarin ta kwantar wa mutanen hankali amma suka cigaba da yi mata ihun 'ba ma so'.

Sanata Philip Aduda, mai wakiltar Abuja a Majalisar Wakilai na Tarayya, ya fice daga wurin taron cikin fushi.

Kara karanta wannan

Zargin safara: Yadda Abba Kyari ya yi aiki da kungiyar dillalan kwayoyi a Brazil, NDLEA

Jami'an tsaro a wurin sun gaza kula da dandazon mutanen da suka fara ihun a wurin taron, rahoton Daily Trust.

Daga nan, ministan ta ajiye abin magana, sannan ta zaga ta gaisa da wasu manyan baki kafin ta bar wurin.

Kwamishinan INEC ya mika satifiket ga zababun ciyamomi

Daga bisani, kwamishinan zaben na INEC, ya mika shaidar lashe zaben ga ciyamomin AMAC, Kwali, Gwagwalada, Bwari da Kuje.

Yayin da ya ke taya ciyomomin murna, Bello, ya bukaci masu ruwa da tsaki su hada kai da INEC domin ganin an yi zaben 2023 lafiya.

Ya yi kira ga shugabannin jam'iyya wu wayar da kan magoya bayansu su karbi katin PVC.

Buhari: Da zarar na kammala wa'adin mulki na zan koma gona ta a Daura in tare

A wani labarin, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya na da kudirin komawa gonarsa ta Daura, mahaifarsa da ke jihar Katsina, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Mun fi karfin mataimakin shugaban kasa, dole a ba mu kujerar shugaban kasa - Kungiyar Ibo

Shugaban kasa ya furta hakan ne a Istanbul, kasar Turkiyya inda aka shirya masa bikin zagayowar ranar haihuwarsa ba tare da saninsa ba a ofishin jakadancin Najeriya da ke kasar.

Buhari ya na kasar Turkiyya yanzu hakan don halartar wani taro inda har ranar haihuwarsa ta zagayo, ya cika shekaru 79 kenan a ranar Juma’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164