APC Ta Yi Rashi Yayinda Ƙanin Gwamna, Buhari, Da Wasu Mutane Da Dama Suka Koma PDP
- Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta kara karfi a Jihar Niger a yayin da ta karbi sabbin mambobi da suka baro APC
- Aminu, kanin Gwamna Abubakar Sani Bello, Abubakar Buhari da wasu da dama sun fice daga APC gabanin zaben shekarar 2023
- Shugaban jam'iyyar PDP na mazabar Kontagora Central, Umar Hassan, ne ya karbi sabbin mambobin, ya kuma basu katinsu na PDP
Niger - Wasu dandazon mutane sun sake ficewa daga jam'iyyar All Progressives Congress, APC a jihar Niger sun koma PDP cikinsu har da Gwamna Abubakar Sani Bello.
Kanin Bello, Aminu, shahararren dan siyasa a Niger North, Abubakar Buhari da wasu da dama sun fice daga APC sun koma babban jam'iyyar adawa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sabbin wadanda suka sauya shekan, a cewar wani rahoto da New Telegraph ta wallafa, sun karbi katinsu na zama mambobin PDP daga hannun shugaban jam'iyyar na mazabar Kontgora Central, Umar Hassan.
An gano cewa kanin gwamnan, Aliyu daga Kontagora Central da Buhari sun karbi katinsu na zama yan jam'iyyar PDP.
Yahaya Abdullahi Ability, shugaban yankin Niger North, ya yi maraba da mutanen biyu da suka dawo PDP. A jawabinsa, Ability, ya bukaci su jajirce don ganin PDP ta yi nasara.
Asali: Legit.ng