IBB ga 'yan siyasa: Kar ku yi wasa da hadin kan 'yan Najeriya
- Gabannin zaben 2023, tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida ya bayar da muhimmiyar shawara ga yan siyasar kasar
- IBB ya bayyana cewa duk rintsi duk wuya kada su kuskura su yi wasa da hadin kan yan Najeriya
- Ya bayar da shawarar ne a lokacin da mai neman takarar shugaban kasa, Prince Adewole Adebayo, ya ziyarce shi a gidansa da ke Hilltop a garin Minna
Niger - Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, ya shawarci shugabannin siyasa da kada su yi wasa da hadin kan kasar duk rintsi.
Babangida ya bayar da shawarar ne a lokacin da ya karbi bakuncin wani mai neman takarar shugaban kasa, Prince Adewole Adebayo, wanda ya kai masa ziyara a gidansa da ke hilltop, Minna.
Adebayo, wanda ya kafa gidan talbijin na Kaftan, ya fada wa manema labarai bayan ganawarsu cewa tsohon shugaban kasar ya shawarce shi da kada ya yi wasa da hadin kan kasar, jaridar Leadership ta rahoto.
Dalilin ziyarar da ya kaiwa IBB
Mai neman takarar a karkashin Third Force ya ce ya je Minna ne domin neman goyon baya, sa albarka, addu’o’i da kuma shawarar IBB kan aniyarsa ta neman shugabancin kasar a zaben 2023.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Dan siyasar ya ce tsohon shugaban kasar ya bayyana bukatar inganta kowane zabe a Najeriya ta yadda zai fi na baya domin karfafa damokradiyyar kasar, kamfanin dillancin labaran Najeriya ta rahoto.
Ya ce:
“Tsohon shugaban kasa Babangida ya yarda cewa kada mu yi wasa da hadin kan kasar duk rintsi duk wuya. Ya shawarce ni cewa idan ina son yin nasara a matsayin shugaban Najeriya, toh dole ne in kafa karamin Najeriya a kowane lokaci, ko da a gidana ne.
“Ya ce ko a cikin harkokinka na cikin gida, idan mutum ya leka sai ya ga wata karamar Najeriya da aka kafa a can. Ya kara da cewa ko a tunanin ka, idan ka kadaita, dole ne ka yi tunani gaba daya, ba wani bangare nasa ba. Cewa dole ne ka dauki shawarwari daga dukkan sassan kasar.”
2023: Bayan Atiku da Tinubu, wani ɗan takarar shugaban ƙasa ya ziyarci IBB a Minna
A gefe guda, mun kawo cewa mai neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Sam Ohuabunwa a ranar Alhamis ya kai wa tsohon shugaban kasar Najeriya, Ibrahim Babangida ziyara a gidansa na Hilltop da ke Minna, Jihar Neja, Channels TV ta ruwaito.
Yayin tattaunawa da manema labarai, Ohuabunwa ya ce babbar kalubalen da Najeriya take fuskanta shi ne rashin ayyukan yi wanda a cewarsa shi yake janyo rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki a kasa.
Ohuabunwa ya samu ganawa da mambobin jam’iyyar PDP na jihar a babban ofishin jam’iyyar, ya ce ya je Jihar Neja ne don neman shawarwarin Babangida da mambobin jam’iyyar na Jihar Neja sakamakon zaben shugaban kasa na 2023 da ke karatowa.
Asali: Legit.ng