Kicibus: Hotunan gamuwar Ganduje da Kwankwaso a filin jirgi sun bar baya da kura
- Gwamnan jihar Kano, Ganduje ya sake gamuwa da Kwankwaso a filin jirgin sama a karo na biyu a jihar Sokoto
- A baya Ganduje ya gana da Kwankwaso, inda suka gaisa a filin jirgin sama, lamarin da ya jawo cece-kuce da yawa
- A wannan karon ma, an kara samun martanin jama'a kan ganawar Ganduje da Kwankwaso a karo na biyu
Jihar Sokoto - Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya yi kicibus da tsohon gwamnan jihar ta Kano, Dr Rabiu Musa Kwankwaso a filin jirgin sama.
Sanarwar da Legit.ng Hausa ta samo daga gwamnati ta bayyana yadda gwamnan ya gaisa da magajin nasa a jihar Sokoto, yayin da suka hadu a filin jirgin Sultan Abubakar III a jihar ta Sokoto.
Rahoton ya ce Ganduje da Kwankwaso sun gana ne a ranar 13 ga watan Fabrairu.
Sanarwar da gidan gwamnatin Kano ta fitar ta shafin Facebook ta ce:
"Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, kenan yayin da suke gaisawa da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso a filin Jirgin sama na Sultan Abubakar lll a Jihar Sokoto."
Kalli hotunan:
Sai dai, bayan yada hotunan, jama'a sun yi martani, inda da dama suka bayyana yadda suka ji ganin yadda 'yan siyasar suka hadu.
Gamuwar tasu dai ta zo ne duk da yadda ake ganin akwai 'yar tsama tsakanin Ganduje da Kwankwaso.
Martanin jama'a
Ga kadan daga martanin da Legit.ng Hausa ta tattaro a karkashin rubutu da hotunan da aka yada a kafar Facebook kamar haka:
Abdurrashid Assalafiyyah Salaf ya ce:
"Masha'allah kaga na gwagwo babu damuwa a kansa."
Muhammad Modibbo kuwa cewa ya yi:
"Kano ta GANDUJE ce."
Aminu Salisu shi kuwa cewa ya yi:
"Allah ya karawa mai girma gwamna lfy, nisan kwana, da jagoranci nagari."
Bala Abdu Maitsidau ya yi martani da cewa:
"Haka siyasa take sir."
Sani Badamasi Mohammed ya ce:
"Uban Abba ya matsa fa madugu sauki yake nema."
Elmustorpher Aliyi ya ce:
"Gayyar tsiya abun takaice."
Siyasar Kano: Maganar sulhu tsakanin Kwankwaso da Ganduje ta jawo ana ta ce-ce-ku-ce
A wani labarin daban, Legit.ng Hausa ta tattaro abubuwan da wasu daga cikin masu bibiyar siyasar Kano da ‘yan Kwankwasiyya da tsagin gwamna Ganduje ke fada a Facebook.
Salisu Yahaya Hotoro ya bayyana ra’ayinsa, yace dole ce ta sa Ganduje zuwa gaisuwar, yace idan mai gidansa, Kwankwaso ya amince ayi sulhu, to zai yi biyayya.
"Allah sarki Modibbo, Wallahi ya fara bani tausayi. Watau ya lura dare yana neman yi masa a dawa, sai ya lallabo gida."
Asali: Legit.ng