Da Ɗumi-Ɗumi: Jonathan Ya Goyi Bayan Gwamnan PDP Ya Zama Shugaban Ƙasa a 2023

Da Ɗumi-Ɗumi: Jonathan Ya Goyi Bayan Gwamnan PDP Ya Zama Shugaban Ƙasa a 2023

  • Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan ya saki wata takarda wacce zata iya janyo cece-kuce cikin manyan yan siyasar kasar nan
  • A cewar Jonathan, yana da yakinin dan takarar shugaban kasa, Gwamna Bala Mohammed zai iya shugabantar Najeriya ba tare da samun tangarda ba
  • Tsohon shugaban kasar ya kwatanta Bala, wanda ya rike kujerar ministan Abuja a lokacin yana shugaban kasa, a matsayin mutum jajirtacce kuma tsayayye

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana yakinin sa akan Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi dangane da mulkin kasar nan a 2023, Channels TV ta ruwaito.

Da Ɗumi-Ɗumi: Jonathan Ya Goyi Bayan Gwamnan PDP Ya Zama Shugaban Ƙasa a 2023
Tsohon shugaban kasa Jonathan ya goyi bayan Bala Mohammed ya zama shugaban kasa. Photo credit: Senator Bala Abdulkadir Mohammed
Asali: Facebook

Kamar yadda aka samu rahoton, Jonathan ya yi wannan bayanin ne a ranar Alhamis, 10 ga watan Fabrairu yayin wani taro, inda yace ya san yadda gwamnan yake jajircewa akan yi wa kasa aiki.

Kara karanta wannan

Jonathan: Asalin abin da ya sa na kirkiro makarantun Almajirai a Arewa a mulkina

An yanko daidai inda tsohon shugaban kasar yake cewa:

“Idan har akwai (a matsayin shugaban kasar), sai kana da da.
“Ko wanne uba yana son dan shi ya girma.
“Wadanda suka yi aiki da ni cikin ku, sun san aiki na ne mara muku baya. Duk ‘yan uwa muke. Hakan ne babbar daukakar da za ta same mu.
“Kai jajirtaccen mutum ne mai mayar da hankali a duk inda ya sa kan sa. Kuma bisa dagewa da goyon bayan ‘yan Najeriya, za ka iya zama shugaban kasa.”

Legit.ng ta kula da cewa Gwamna Bala ya rike kujerar ministan Abuja a lokacin da Jonathan yana shugaban kasa.

2023: Jonathan ya nuna gamsuwarsa bisa kwazo na - Gwamna Mohammed

Kazalika, a wani wallafa na Facebook da Legit.ng ta gani, Gwamna Mohammed ya ce tsohon mai gidansa ya nuna gamsuwarsa cewa zai iya shugabancin Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaban NNPC ya bayyana wadanda suka shigo da rubabben fetur daga kasar waje

Ya rubuta cewa:

"Yau na ziyarci tsohon shugaban kasa Dr Goodluck Ebele Jonathan a gidansa da ke Abuja. Na je in sanar da shi niyya ta na yin takarar ofishin shugaban kasa a zabe mai zuwa.
"Ya bayyana gamsuwarsa cewa ya yi imanin zan iya biya wa yan Najeriya bukatunsu ta hanyar shugabanci nagari, duba da irin nasarorin da na samu a matsayin Ministan Abuja da kuma yanzu a matsayin gwamna."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164