'Karin bayani: Tsohon gwamna da ya sha kaye a zaɓen fidda gwani ya fice daga PDP

'Karin bayani: Tsohon gwamna da ya sha kaye a zaɓen fidda gwani ya fice daga PDP

  • Tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Segun Oni ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP
  • Adebaya Jackson, shugaban kungiyar yakin neman zaben Segun Oni ne ya sanar da hakan a ranar Asabar
  • Segun Oni ya fice daga PDP ne jim kadan bayan ya sha kaye a zaben fidda gwani na takarar gwamna inda ya zo na biyu

Ekiti - Gabanin zaben gwamnan Jihar Ekiti ta ranar 18 ga watan Yuni, tsohon Gwamna Segun Oni, kuma wanda ya zo na biyu a zaben cikin gida da aka kammala a baya-bayan nan ya fice daga jam'iyyar PDP.

Adebaya Jackson, Direktan Watsa Labarai na Kungiyar Kamfen ta Segun Oni Movement ne ya tabbatarwa The Nation hakan a Ado Ekiti, Jihar Ekiti a ranar Asabar.

Yanzu-Yanzu: Tsohon gwamna da ya sha kaye a zaben fidda gwani ya fice daga PDP
Tsohon Gwamna Segun Oni ya fice daga PDP gabanin zaɓen jiharsa. Hoto: The Cable
Source: Twitter

Sai dai a halin yanzu Oni bai bayyana jam'iyyar da zai koma ba bayan ficewar daga PDP.

Kara karanta wannan

Dukiyar sata: Yadda Ministan Buhari ya lallaba, ya ba kamfani kwangilar makudan Biliyoyi

Amma ana hasashen tsohon gwamnan zai iya shiga jam'iyyar AProgressives Grand Alliance (AGPA) don samun damar fafatawa a zaben na gwamna, The Cable ta ruwaito.

Sai dai Jackson ya ce tsohon gwamnan zai sanar da jam'iyyar da zai koma a ranar Talata inda za a saka sunansa kafin ranar rufe mika sunayen masu takarar gwamnan da za a yi a ranar 18 ga watan Yuni.

Ya ce Oni ya amsa kira da matsin lambar da mafi yawancin mutanen Ekiti ke masa ne na cewa ya dawo gidan gwamnati ko ma a wace jam'iyya ne.

Tsohon sakataren watsa labarai na PDPn ya yi nuni da cewa tsohon gwamnan zai fice daga PDPn din tare da dubban magoya bayansa.

Kalamansa:

"Engr. Segun Oni ya yi murabus daga PDP. Dukkan mutanen Ekiti sun nuna suna son Oni ya dawo gidan gwamnati ko a wacce jam'iyya ne. Kuma ya amsa kirarsu.
"Hasali ma, farin jininsa ne ya ke daukaka darajar PDP a Jihar Ekiti. Kuma tunda PDP ta yanke shawarar kashe kanta, mun yanke shawarar mu fice.

Kara karanta wannan

Wuyan Abokin takarar Atiku a zaben 2019 ya yi kauri, zai nemi Shugaban kasa a 2023

"Mutanen Ekiti ba za su rabu da Oni ba saboda ba su ga wani mutum dai zai musu irin aikin da Oni ke musu ba.
"Don haka, muryar mutanen ne ba na kowa ba. A yanzu, PDP da APC za su yi takara ne da mutanen Ekiti. Kuma wakilin mutanen Ekiti shine Engr. Oni."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164