Takara a 2023: Tinubu ba a bakin komai yake, ba zai iya hana ni cimma burina ba, Sanatan APC
- Sanata Kalu ya yi ikirarin cewa ya shirya kalubalantar jagoran APC, Bola Tinubu, wajen cimma burinsa na zama shugaban ƙasa na gaba
- Sanatan yace duk abin da Tinubu ke tunƙaho da shi a siyasan ce to shima ya taka wannan mukamin kuma yana da mutane
- Sai dai yace ba zai iya hana Tinubu takara ba, amma za su haɗu filin zaɓen fidda gwani, inda za'a yi ta ƙare
Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa, Sanata Orji Uzor Kalu, yace tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu, bai kai ya hana shi cimma burinsa na gaje kujerar Buhari ba.
Sanatan ya yi wannan furucin ne ranar Jumu'a yayin da yake fira da kafar watsa labarai ta Channels tv cikin shirin Siyasa a Yau.
Yayin firar, sanatan ɗan jam'iyyar APC ya yi tsokaci kan manufar da yake da ita ga Najeriya idan ya samu nasarar darewa mulkin shugaban Najeriya
Da aka tambaye shi ko yana ganin Tinubu zai iya zame masa cikas a wajen cimma burinsa na zama shugaban ƙasa, Kalu ya amsa da cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Aa, kuma ni ba zan zame masa barazana ba. Amma duk lokacin da muka fita fagen fafatawa a Eagles Square, za'a warware matsalar."
"Amma ina son ƙusani siyasa ba ta dogara kacokan a kan kuɗi ba, ta dogara ne ga mutanen da zaka mulka. Mutanen dake dukka sassan Najeriya shida, kuma muna tare da su."
Siyasar tsofaffin gwamnonin biyu
Kalu da Tinubu duka jigogin jam'iyyar APC ne, kuma sun rike mukamin gwamna a jihohinsu daga shekarar 1999 zuwa 20017.
A watan Nuwamban shekarar da ta gabata, Bola Tinubu, ya ziyarci Kalu a gidansa dake Abuja, kuma manyan mutanen biyu sun tattauna amma a sirrin ce.
Duk da cewa Kalu ya amince cewa lokacin da Tinubu ya ziyarce shi ba shi ba kudirin neman kujera lamba ɗaya, amma akwai dalilan da yasa ya canza tunani.
Wane dalilai ne suka sa ya fito takara?
Daily Trust ta rahoto Sanata Kalu yace:
"Na gaya wa Tinubu cewa ba zan shiga neman takara ba, wannan itace gaskiya.Wani yanayi ne da ya taso daga Kudu-Gabas, Kudu-Yamma, Arewa ta tsakiya, Arewa ta yamma da Arewa ta gabas, su ne suka san na shiga tseren."
"Na rike gwamna a lokacin da shi ma yake kan kujerar gwamna, ba abu ne mai wahala ba wajen fafatawa da kowa."
"Zamu haɗu a filin Eagle Square, a nan za'a yi ta ƙare, dan haka ba abu ne mai wahala ba."
Game da sanar da Buhari, Sanata Kalu ya bayyana cewa ganawarsa ta karshe da shugaba Buhari ba siyasa suka tattauna ba, sun maida hankali ne kan halin da ƙasa ke ciki.
A wani labarin kuma Shugaba Buhari ya tabbatarwa yan Najeriya cewa cikin watanni masu zuwa za su ga gagarumin canji na cigaba
Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari , ya tabbatar wa yan Najeriya cewa yana sane da alƙawurran da ya ɗauka a shekarar 2015.
Shugaban yace cikin yan watanni kaɗan masu zuwa, mutane za su ga gagarumin canji a arewa maso gabashin Najeriya.
Asali: Legit.ng