APC ta aike wa INEC sanarwar za ta yi gangamin zaben shugabannin jam'iyya na kasa

APC ta aike wa INEC sanarwar za ta yi gangamin zaben shugabannin jam'iyya na kasa

  • A hukumance, jam'iyya mai mulki ta APC ta aike wa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa sanarwar za ta yi zaben shugabannin jam'iyyar na kasa
  • Kamar yadda wasikar ta bayyana, APC ta aika wasikar a ranar 2 ga Fabrairu kuma INEC ta same ta a ranar 3 ga watan Fabrairu
  • APC cike da girmamawa ta sanar da INEC kuma ta ke kira gare ta da ta shirya jami'an ta domin lura da zaben da za a yi ranar 26 ga wata

Shugaban Kwamitin rikon kwarya na jam'iyya mai mulki, Mai mala Buni, ya sanar da hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, kan hukuncinsu na yin gangamin zaben shugabannin jam'iyyar a ranar da suka tsayar.

Taron gangamin zaben shugabannin jam'iyya mai mulkin za a yi shi ne a ranar 26 ga watan Fabrairu kuma jam'iyyar ta na da damar kai sanarwar ta ga INEC ne har zuwa ranar 5 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: APC ta tabbatar da ranar gudanar da babban taronta na kasa, 26 ga watan Fabrairu

APC ta aike wa INEC sanarwar za ta yi gangamin zaben shugabannin jam'iyya na kasa
APC ta aike wa INEC sanarwar za ta yi gangamin zaben shugabannin jam'iyya na kasa. Hoto daga channelstv.com
Source: UGC

Kamar yadda wasikar da Channels TV ta gani mai taken "Sanarwa kan gangamin zaben jam'iyya na kasa" kuma shugaban kwamitin, Mai Mala Buni da sakataren kwamiti John Akpanudoedehe suka saka hannu, sun sanar da hukumar zaben hukuncin da suka yanke a ranar 2 ga watan Fabrairu.

Hatimin da aka buga a wasikar ya bayyana cewa hukumar zaben mai zaman kanta ta kasa ta samu wasikar a ranar 3 ga watan Fabrairun 2022.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Channels Tv ta ruwaito cewa, wani bangare na wasikar ya ce:

"Muna sanar da hukumar cewa jam'iyyar mu ta shirya yin gangamin zaben shugabannin jam'iyyar na kasa ranar 26 ga watan Fabrairun 2022.
"Wannan na bayyana sanarwar mu kamar yadda sashi na 85 na dokokin zaben gyararru na 2010 suka tanada.
“Muna bukatar ku shirya jami'an ku domin su lura da zaben yadda ya dace. A yayin da muke fatan samun hadin kan ku, muna tabbatar muku da tsananin girman ku da muke gani," takardar tace.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An tsaurara tsaro a sakateriyar APC yayin da ake rantsar da shugabannin jihohi

Daga karshe: Bayan dogon cece-kuce, APC ta saka ranar taron gangami a Fabrairu

A wani labari na daban, jam’iyyar APC mai mulki ta tsayar da ranar 26 ga watan Fabrairun bana domin gudanar da taron gangaminta na kasa, Vanguard ta ruwaito.

Shugaban kwamitin tsare-tsare na rikon kwarya (CECPC), Gwamna Mai Mala Buni ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Abuja a taron mata da jam’iyyar ta shirya.

IGP Alkali Baba yace sam bai da labarin hukumomin kasar Amurka sun gabatar da takarda, suna neman a mika masu jami’in ‘dan sandan Najeriyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng