Shugaban kasa a 2023: Okorocha ya gana da Buhari kan kudirinsa na son zama magajinsa

Shugaban kasa a 2023: Okorocha ya gana da Buhari kan kudirinsa na son zama magajinsa

  • Sanata mai wakiltan Imo ta yamma a majalisar dattawa, Sanata Rochas Okorocha ya sa labule da shugaban kasa Muhammadu Buhari
  • Okorocha ya gana da Buhari ne domin sanar da shi aniyarsa ta son tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023
  • Tsohon gwamnan ya kuma ce ya fada ma shugaban kasar irin rashin adalcin da EFCC ke yi masa

Abuja- Gabannin babban zaben 2023, Sanata Rochas Okorocha ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa a ranar Alhamis, 3 ga watan Fabrairu.

Jaridar Leadeship ta rahoto cewa sanatan ya ziyarci shugaban kasarne a kan kudirinsa na son tsayawa takarar shugaban kasa a babban zaben 2023.

Shugaban kasa a 2023: Okorocha ya gana da Buhari kan kudirinsa na son zama magajinsa
Shugaban kasa a 2023: Okorocha ya gana da Buhari kan kudirinsa na son zama magajinsa Hoto: Aso Rock Villa
Asali: Facebook

A cewar tsohon gwamnan na jihar Imo, ya sanar da Shugaba Buhari cewa ya kamata a saka dukkanin jam’iyyu hudu da suka dunkule suka zama jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a harkokin babban taron jam’iyyar mai zuwa.

Kara karanta wannan

Takarar 2023: Atiku, Saraki, Tambuwal sun karbi mummunan labari daga jigo a Kudu

Okorocha, wanda ke wakiltan Imo ta yamma a majalisar dokokin tarayya, ya kara da cewar ya kuma sanar da shugaban kasar game da rashin adalcin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ke yi masa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Okorocha: Na yi gwamna ban samu komai ban da karin talauci, sanata bayyana halin da yake ciki

A baya mun ji cewa mai aniyar zama shugaban kasa kuma jigon jam'iyyar Progressives Congress (APC), Rochas Okorocha, ya ce kasancewarsa gwamnan jihar Imo bai kara masa komai ba sai talauci.

Tsohon gwamnan, wanda ya kasance sanata mai wakiltan Imo ta yamma a yanzu haka, ya ce yana bin gwamnatin jihar bashin naira biliyan 8 na tsaro.

Ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 31 ga watan Janairu, yayin da ya bayyana a shirin Channels TV na Politics Today wanda Punch ta sanya ido.

Kara karanta wannan

Buhari ba zai iya tafiyar mota babu shiri ba, Fadar shugaban kasa ta yi wa PDP martani kan ziyarar Zamfara

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng