Zaben 2023: Jerin mutum 7 da Buhari ya nada a hukumar INEC, majalisa ta tabbatar
- Majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da sunayen mutane bakwai da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada
- Jerin wadanda aka tabbatar sun hada da kwamishinonin shiyyoyin siyasa ta tarayyar Najeriya, kamar yadda rahotanni suka tabbatar
- A halin da ake ciki, bukatar tabbatar da hakan a cewar wani Sanata na jam’iyyar APC, ya yi dai dai da kundin tsarin mulkin 1999
Abuja- Majalisar dattawa ta tabbatar da sunayen mutane bakwai da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada a matsayin kwamishinonin zabe na kasa kuma shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).
Tabbatar da wadanda aka nadan a ranar Laraba, 2 ga watan Fabrairu, ya biyo bayan nazarin rahoton kwamitin majalisar dattawa kan INEC, inji rahoton Punch.
Wadanda aka tabbatar
- Mal. Mohammed Haruna (Niger – Kwamishinan Arewa ta Tsakiya)
- Mrs May Agbamuche-Mbu (Delta – Kwamishinan Kudu maso Kudu)
- Ukeagu Kenneth Nnamdi (Abia – Kwamishinan Kudu maso Gabas)
- Major General A. B. Alkali (Rtd) – (Adamawa - Kwamishinan Arewa maso Gabas).
- Farfesa Rhoda H. Gumus (Bayelsa – Kwamishinar Kudu maso Kudu)
- Mista Sam Olumekun (Ondo – Kwamishinan Kudu maso Yamma)
- Olaniyi Olaleye Ijalaye (Ondo – Kudu maso Yamma).
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shugaban kwamitin Sanata Kabiru Gaya a nasa jawabin, ya tunatar da cewa shugaban kasa ne ya gabatar da bukatar ta tabbatar da jami'an
Hakazalika, ya ce hakan ya yi daidai da sashe na 153(1) (f) na kundin tsarin mulkin kasa, kuma bisa tanadin sashe na 154( 1) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya, 1999 (wanda aka yiwa kwaskwarima), Vanguard ta kara da cewa.
Ya bayyana cewa kwamitin ya samu takardar koke daga kungiyar dattawan jihar Taraba game da nadin da aka yi wa Manjo Janar A. B. Alkali (Rtd) kan “da alamun rashin daidaito a zaben nadin”.
Matsayar 'yan majalisa
‘Yan majalisar da suka hada da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ovie Omo-Agege da Sanata James Manager, sun yi magana sosai kan cancanta da amincin wadanda Shugaban kasa ya nada.
Matsayar Lawan
Shugaban Majalisar Dattawa, a jawabinsa bayan an tabbatar da wadanda aka nada, ya taya su murna tare da lura da cewa babban zaben 2023 zai tabbatar da ingancinsu.
Ya kara da cewa majalisar dokokin kasar za ta marawa hukumar zabe baya domin ganin an gudanar da sahihin zabe a shekarar 2023.
A wani labarin, jaridar The Cable ta ruwaito cewa majalisar dattawa ta tabbatar da Rhoda Gumus a matsayin kwamishinar hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) daga kudu maso kudu.
Hakan na zuwa ne duk da rade-radin da ake yi na cewa Gumus wacce aka zaba daga jihar Bayelsa ta kasance mamba a jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Kafin rantsar da Gumus, kungiyar kare hakkin dan adam ta HURIWA, ta mika takardar korafi gaban shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan kan nadin nata.
Asali: Legit.ng